MAL 1

Ubangiji Yana Ƙaunar Yakubu

1 Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya ba Malakai ya faɗa wa jama’ar Isra’ila.

2 Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunarku.”

Amma ku kuka amsa kuka ce, “Ta yaya kake ƙaunarmu?”

Ubangiji ya amsa, ya ce, “Ashe, Isuwa da Yakubu ba ‘yan’uwan juna ba ne? Amma zuriyar Yakubu nake ƙauna.

3 Na ƙi Isuwa da zuriyarsa, na hallaka ƙasarsa ta kan tudu, wurin zamansa kuwa na ba namomin jeji.”

4 Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.”

Sa’an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al’ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”

5 “Da idanunku za ku ga wannan, za ku kuwa ce, Allah mai girma ne yake a ƙasar da ba ta Isra’ila ba ce!”

Ubangiji Ya Tsauta wa Firistoci

6 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’

7 Yadda kuka yi ke nan. Kun miƙa haramtacciyar hadaya ta abinci a kan bagadena, sa’an nan kuna cewa, ‘Ta ƙaƙa muka raina ka?’ To, zan faɗa muku, don kun ƙazantar da bagadena.

8 Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa’ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

9 To, firistoci ku gwada, ku roƙi Allah domin ya yi mana alheri. Ai, ba zai amsa addu’arku ba, wannan kuwa laifinku ne. Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.

10 “Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

11 “Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko’ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

12 “Amma ku kun raina ni da yake kuka ce bagadena ba kome ba ne, kuna raina abincin da kuke ajiyewa a kai.

13 Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?

14 La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyun dabbobi da ya alkawarta zai ba ni daga cikin garkensa ya kuwa miƙa mini hadaya ta haramtacciyar dabba. Gama ni babban Sarki ne, dukan al’ummai kuwa suna jin tsoron sunana, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”