MAL 4

Ranar Ubangiji Mai Zuwa

1 “Duba rana tana zuwa, sa’ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

2 Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar ‘yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.

3 Za ku tattake mugaye, gama za su zama kamar ƙura a ƙarƙashin ƙafafunku, a ranan nan da zan aikata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

4 “Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama’ar Isra’ila su kiyaye.

5 “Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.

6 Zai sāke kawo iyaye da ‘ya’ya wuri ɗaya, da ba don haka ba, da sai in zo in hallaka ƙasar.”