MAR 3

Mai Shanyayyen Hannu

1 Sai ya sāke shiga majami’a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu.

2 Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.

3 Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.”

4 Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru.

5 Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.

6 Da Farisiyawa suka fita, nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.

Taro Mai Yawa a Bakin Teku

7 Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya,

8 da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi.

9 Don gudun kada taron ya mammatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda,

10 saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi.

11 Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa’ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.”

12 Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.

Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu

13 Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa.

14 Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa’azi.

15 Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu.

16 Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus,

17 da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan’uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato ‘ya’yan tsawa.

18 Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan’ane,

19 da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi.

Yesu da Ba’alzabul

Sa’an nan ya shiga wani gida.

20 Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci.

21 Da ‘yan’uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.”

22 Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba’alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”

23 Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan?

24 Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba.

25 Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba.

26 Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo.

27 Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa’an nan kuma ya washe gidansa.

28 “Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa ‘yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta,

29 amma fa, duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.”

30 Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”

Uwar Yesu da ‘Yan’uwansa

31 Sa’an nan uwa tasa da ‘yan’uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je.

32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da ‘yan’uwanka suna nemanka a waje.”

33 Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da ‘yan’uwana?”

34 Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da ‘yan’uwana!

35 Ai, kowa ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗan’uwana, ita ce ‘yar’uwata, ita ce kuma tsohuwata.”