MAR 6

An Ƙi Yesu a Nazarat

1 Ya tashi daga nan ya koma garinsu, almajiransa kuwa suka bi shi.

2 Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami’a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu’ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!

3 Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan’uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? ‘Yan’uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.

4 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin ‘yan’uwansa, da kuma gidansu.”

5 Bai ko iya yin wata mu’ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkar da su.

6 Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.

Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.

Yesu Ya Aiki Sha Biyu Ɗin Nan

7 Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.

8 Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,

9 amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.

10 Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.

11 Duk inda aka ƙi yin na’am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.”

12 Haka fa, suka fita, suna wa’azi mutane su tuba.

13 Suka fitar da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkar da su.

Mutuwar Yahaya Maibaftisma

14 Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu’ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”

15 Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.”

16 Amma da Hirudus ya ji haka, sai ya ce, “Yahaya, wanda na fille wa kai, shi ne aka tasa.”

17 Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan’uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.

18 Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, “Bai halatta ka zauna da matar ɗan’uwanka ba.”

19 Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,

20 don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa’ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.

21 Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki.

22 Da ‘yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Roƙe ni kome, sai in ba ki.”

23 Ya kuma rantse mata, ya ce, “Kome kika roƙe ni zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

24 Ta fita, ta ce wa uwa tata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.”

25 Nan da nan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa, ta roƙe shi, ta ce, “Ina so yanzu yanzu ka ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi.”

26 Sai sarki ya yi baƙin ciki gaya, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ba ya so ya hana ta.

27 Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi umarni a kawo kan Yahaya. Ya tafi ya fille wa Yahaya kai a kurkuku,

28 ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa to ba uwa tata.

29 Da almajiran Yahaya suka ji labari, sai suka zo suka ɗauki gangar jikinsa, suka sa ta a kabari.

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

30 Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar.

31 Ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita a wurin da ba kowa, ku ɗan huta.” Domin mutane da yawa suna kaiwa suna kawowa, ko damar cin abinci ma, manzannin ba su samu ba.

32 Sai suka tafi cikin jirgi wurin da ba kowa, su kaɗai.

33 Ashe, mutane da yawa sun ga tafiyarsu, sun kuwa shaida su, suka fa dunguma ta tudu daga garuruwa duka, suka riga su zuwa.

34 Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.

35 Kusan faɗuwar rana sai almajiransa suka zo gare shi, suka ce masa, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta kusa fāɗuwa.

36 Sai ka sallame su, su shiga karkara da ƙauyuka na kurkusa, su saya wa kansu abinci.”

37 Amma ya amsa musu ya ce, “Ku ku ba su abinci mana.” Sai suka ce masa, “Wato mu je mu sayo gurasa ta dinari metan, mu ba su su ci?”

38 Ya ce musu, “Gurasa nawa gare ku? Ku je ku dubo.” Da suka binciko suka ce, “Ai, biyar ne, da kifi biyu.”

39 Sa’an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna ƙungiya ƙungiya a ɗanyar ciyawa.

40 Haka suka zauna jeri jeri, waɗansu ɗari ɗari, waɗansu hamsin hamsin.

41 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama’a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.

42 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi,

43 har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin gurasar da na kifin.

44 Waɗanda suka ci gurasan nan kuwa maza dubu biyar ne.

Yesu na Tafiya a kan Ruwan Teku

45 Nan da nan ya sa almajiransa su shiga jirgi su riga shi hayewa zuwa Betsaida, kafin ya sallami taron.

46 Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse domin ya yi addu’a.

47 Da magariba ta yi, jirgin na tsakiyar teku, Yesu kuwa na nan kan tudu shi kaɗai,

48 da ya ga suna fama da tuƙi, gama iska na gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su,

49 amma da suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka zaci fatalwa ce, suka yi kururuwa,

50 domin duk sun gan shi, sun kuwa firgita. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, ni ne, kada ku ji tsoro.”

51 Sa’an nan ya shiga jirgi wurinsu, iska kuma ta kwanta. Sai mamaki ya kama su ƙwarai,

52 don ba su fahimci al’amarin gurasan nan ba, saboda zuciyarsu ta taurare.

Yesu Ya Warkar da Marasa Lafiya a Janisarata

53 Da suka haye, suka isa ƙasar Janisarata, suka ɗaure jirgin a gaɓa.

54 Da fitarsu daga jirgin sai mutane suka shaida shi.

55 Suka gama ƙasar da gudu, suka fara ɗaɗɗauko marasa lafiya a kan shimfiɗunsu zuwa duk inda suka ji yake.

56 Duk inda ya shiga kuma, birni ko ƙauye ko karkara, sukan kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi su taɓa ko ma da gezar mayafinsa ma. Iyakar waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.