MAT 23

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura da Farisiyawa

1 Sa’an nan Yesu ya yi wa jama’a da almajiransa magana, ya ce,

2 “Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa.

3 Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.

4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.

5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.

6 Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami’u,

7 a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.

8 Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ‘yan’uwa ne.

9 Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama.

10 Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu.

11 Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku.

12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.

13 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. [

14 Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu’a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.]

15 Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.

16 “Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

17 Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?

18 Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

19 Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar?

20 Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa.

21 Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa.

22 Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.

23 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na’ana’a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.

24 Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!

25 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.

26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.

27 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.

28 Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.

29 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai.

30 Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’

31 Ta haka kuka shaidi kanku ku ne ‘ya’yan masu kisan annabawa.

32 To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!

33 Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?

34 Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami’unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.

35 Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.

36 Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”

Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima

37 “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara ‘yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe!

39 Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”