MAT 4

Shaiɗan Ya Gwada Yesu

1 Sa’an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi.

2 Da ya yi azumi kwana arba’in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.

3 Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”

4 Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,

‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,

Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”

5 Sa’an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,

6 ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,

‘Zai yi wa mala’ikunsa umarni game da kai,’

da kuma

‘Za su tallafe ka,

Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

7 Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

8 Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.

9 Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”

10 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,

‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,

Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

11 Sa’an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala’iku sun zo suna yi masa hidima.

Yesu Ya Fara Hidima a Galili

12 To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.

13 Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,

14 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,

15 “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali,

Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun,

Da kuma ƙasar Galili ta al’ummai,

16 Mazaunan duhu sun ga babban haske,

Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta,

Haske ya keto musu.”

17 Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa’azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”

Yesu Ya Kira Masunta Huɗu

18 Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu ‘yan’uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.

19 Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”

20 Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.

21 Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma ‘yan’uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.

22 Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.

Yesu Ya Hidimanta wa Mutane Masu Yawa

23 Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami’unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.

24 Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

25 Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.