ROM 4

Misali na Ibrahim

1 To, me ke nan za mu ce a game da Ibrahim, kakan kakanninmu?

2 Gama in da Ibrahim ya sami kuɓuta ta aikinsa na lada, ashe kuwa, yana da abin yin taƙama ke nan, amma fa ba a gaban Allah ba.

3 To, me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”

4 Wanda yake aikin lada, ladarsa ba kyauta ba ce, sakamakon aikinsa ce.

5 Wanda ba ya aikin lada, amma yana dogararsa ga Allah, wanda yake kuɓutar da masu laifi, akan lasafta bangaskiyar nan tasa adalci ce.

6 Haka kuma Dawuda ya yi maganar albarkar da aka yi wa mutumin da Allah yake lasafta adalci a gare shi, ba don ya yi aikin lada ba,

7 da ya ce,

“Albarka tā tabbata ga waɗanda aka yafe wa laifofinsu,

Waɗanda kuma aka shafe zunubansu,

8 Albarka tā tabbata ga wanda faufau Ubangiji ba zai lasafta zunubansa ba.”

9 To, wannan albarka, masu kaciya ne kawai ake yi wa, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Gama abin da muke cewa shi ne, “Aka lasafta bangaskiyar Ibrahim adalci ce a gare shi.”

10 To, a cikin wane hali aka lasafta masa ita? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa tun ba a yi ba? Ai, tun ba a yi ba ne, ba bayan da aka yi ba.

11 Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba,

12 haka kuma yă zama uban masu kaciya, waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba, har ma suna bin hanyar bangaskiyar nan ta kakanmu Ibrahim, wadda shi ma ya bi, tun ba a yi masa kaciya ba.

Tabbatar da Alkawari ta Wurin Bangaskiya

13 Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa, cewa zai zama magājin duniya, ba ta Shari’a aka yi masa ba, amma domin ya ba da gaskiya ne, shi ya sa Allah ya karɓe shi mai adalci ne.

14 In dai masu bin Shari’a su ne magāda, ashe, bangaskiya ta zama banza ke nan, alkawarin nan kuma ya wofinta,

15 don Shari’a tana jawo fushin Allah. A inda ba Shari’a kuwa, ba keta umarni ke nan.

16 Saboda haka al’amarin ya dogara ga bangaskiya, domin yă zama bisa ga alheri, don kuma a tabbatar da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari’a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda suke da bangaskiya irin Ibrahim, shi da yake ubanmu duka.

17 kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na sa ka uban al’ummai da yawa.” Shi ne kuwa ubanmu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato mai raya matattu, shi ne kuma mai kiran marasa kasancewa kamar sun kasance.

18 Ibrahim kuwa ko da yake ba halin sa zuciya a gare shi, sai ya yi ta sawa, ya gaskata zai zama uban al’ummai da yawa, kamar yadda aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za ta yawaita.”

19 Bangaskiyarsa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi gajiyawar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haihuwa.

20 Ba kuwa wata rashin bangaskiyar da ta sa shi shakkar cikar alkawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa ya yi, yana ɗaukaka Allah,

21 yana haƙƙaƙewa, cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alkawari.

22 Shi ya sa aka lasafta bangaskiyarsa adalci ce a gare shi.

23 To, “lasafta masa” ɗin nan da aka rubuta kuwa, ba saboda Ibrahim kaɗai aka rubuta ba,

24 har saboda mu ma, za a lasafta mana, wato mu da muke gaskatawa da wannan da ya ta da Yesu Ubangijinmu daga matattu,

25 wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi, domin mu sami kuɓuta ga Allah.