W. W. 7

1 Ƙafafunki suna da kyau da takalmi,

Ke mafificiyar budurwa!

Tsarin cinyoyinki kamar aikin gwanin sassaƙa ne.

2 Cibinki kamar finjali ne, wanda bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi a ciki ba.

Kwankwasonki kamar damin alkama ne a tsakiyar bi-rana.

3 Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.

4 Wuyanki kamar hasumiyar hauren giwa ne.

Idonki kamar tafki ne cikin birnin Heshbon,

Kusa da ƙofar Bat-rabbim.

Hancinki kyakkyawa ne kamar hasumiyar Lebanon ta tsaron Dimashƙu.

5 Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel.

Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne,

Yakan kama hankalin sarki.

Daɗin Soyayyar Amarya da Ango

6 Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,

Kina sa ni jin daɗi a rai.

7 Kina da kyan gani kamar itacen dabino,

Mamanki kamar nonnan dabino.

8 Zan hau itacen dabino in tsinko ‘ya’yan.

Mamanki kamar nonnan inabi suke a gare ni.

Numfashinki kamar ƙanshin gawasa ne.

9 Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne.

Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena,

Ya gangara leɓunan masu barci.

10 Ni ta ƙaunataccena ce, yana bukatata.

11 Zo saurayina, bari mu tafi waje,

Mu kwana a karkara.

12 Za mu tashi da sassafe, mu duba kurangun inabi,

Mu ga ko sun fara tohowa,

Ko furanni sun fara buɗewa.

Mu ga ko itatuwan rumman sun yi fure.

A can zan bayyana maka ƙaunata.

13 Za ka ji ƙanshin shuke-shuke

Da na dukan ‘ya’yan itatuwa masu daɗi.

Na adana maka jin daɗi na dā da na yanzu, ya ƙaunataccena.