W. YAH 10

Mala’ika da Ƙaramin Littafi

1 Sa’an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala’ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.

2 Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,

3 ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa.

4 Sa’ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”

5 Sai mala’ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,

6 ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,

7 sai dai a lokacin busa ƙahon da mala’ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.

8 Sa’an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”

9 Sai na je wurin mala’ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”

10 Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala’ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci.

11 Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama’a iri iri, da al’ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”