W. YAH 13

Dabbobi Biyu Ɗin

1 Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.

2 Dabbar da na gani kuwa kamar damisa take, ƙafafunta kamar na beyar, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da kursiyinsa, da ikonsa mai girma.

3 Ɗaya daga cikin kawunanta, an yi masa rauni kamar na ajali, amma rauninsa mai kamar na ajalin nan ya warke. Sai dabbar ta ɗauke wa duk duniya hankali, suna mamaki,

4 har suka yi wa macijin nan sujada, don shi ne ya bai wa dabbar ikonsa, suka kuma yi wa dabbar sujada, suna cewa, “Wa ya yi kama da dabbar nan? Wa kuma zai iya yaƙi da ita?”

5 An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba’in da biyu.

6 Sai ta buɗe bakinta don ta saɓi Allah, ta yi ta saɓon sunansa, da wurin zamansa, da waɗanda suke a zaune a Sama.

7 Aka kuma yardar mata ta yaƙi tsarkaka, ta cinye su. Aka kuma ba ta iko a kan kowace kabila, da jama’a, da harshe, da al’umma.

8 Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.

9 Duk mai kunnen ji, yă ji.

10 Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar.

Kowa kuwa ya yi kisa da takobi, to, kuwa da takobi za a kashe shi lalle.

Wannan yana nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka.

11 Sa’an nan na ga wata dabba na fitowa daga cikin ƙasa. Tana da ƙaho biyu kamar na ɗan rago, maganarta kuwa kamar ta macijin nan.

12 Tana zartar da duk ikon dabbar nan ta farko, a kan idonta, tana kuma sa duniya da duk mazauna a cikinta, su yi wa dabbar nan ta farko sujada, wadda aka warkar mata da rauninta mai kamar na ajali.

13 Tana yin manyan abubuwan al’ajabi, har ma tana sa wuta ta zuba a ƙasa daga sama, a gaban idon mutane.

14 Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al’ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.

15 An kuma yardar mata ta busa wa siffar dabbar nan rai, har siffar dabbar nan ma ta iya yin magana, ta kuma sa a kashe waɗanda suka ƙi yi wa siffar dabbar nan sujada.

16 Har wa yau, sai ta sa a yi wa kowa alama a hannun dama, ko a goshi, manya da yara duka, mawadata da matalauta, ɗa da bawa,

17 har ba mai iya saye ko sayarwa sai ko yana da alamar nan, wato, sunan dabbar nan, ko kuwa lambar sunanta.

18 Wannan abu sai a game da hikima. Duk mai basira ya ƙididdige lambar dabbar nan, don lamba ce ta wani mutum, lambar kuwa ɗari shida ce da sittin da shida.