W. YAH 2

Saƙo zuwa ga Afisa

1 “Sai ka rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.

2 “ ‘Na san ayyukanka, da famarka, da jimirinka, da yadda ba ka iya haƙurce wa mugaye, ka kuma gwada waɗanda suke ce da kansu manzanni, alhali kuwa ba su ba ne, ka tarar na ƙarya ne.

3 Na sani kana haƙuri, kana kuma jimiri saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.

4 Amma ga laifinka, wato, ka yar da ƙaunar da ka yi tun daga farko.

5 Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.

6 Amma a wannan waje kam ka kyauta, kā ƙi ayyukan Nikolatawa, ni ma kuwa na ƙi su.

7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin ‘ya’yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”

Saƙo Zuwa ga Simirna

8 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Simirna haka, ‘Ga maganar wanda yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu, ya kuma sāke rayuwa.

9 “ ‘Na san tsananin da kake sha, da talaucinka (amma bisa ga hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu suke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama’ar Shaiɗan ne.

10 Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.

11 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, mutuwa ta biyu ba za ta cuce shi ba ko kaɗan.’ ”

Saƙo Zuwa ga Birgamas

12 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Birgamas haka, ‘Ga maganar wanda yake da takobi mai kaifi biyu.

13 “ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.

14 Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal’amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra’ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.

15 Haka kai ma kake da waɗansu masu bin koyarwar Nikolatawa.

16 Saboda haka, sai ka tuba. In ba haka ba kuwa, zan zo a gare ka da wuri, in yaƙe su da takobin da yake a bakina.

17 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”

Saƙo Zuwa ga Tayatira

18 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Tayatira haka, ‘Ga maganar Ɗan Allah, mai idanu kamar harshen wuta, mai ƙafafu kamar gogaggiyar tagulla.

19 “ ‘Na san ayyukanka, da ƙaunarka, da bangaskiyarka, da ibadarka, da jimirinka, ayyukanka kuma na yanzu, sun fi na farkon.

20 Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.

21 Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta.

22 To, ga shi, zan jefa ta a gado, masu yin fasikanci da ita kuma zan ɗora musu matsananciyar wahala, sai ko in sun tuba da irin aikinta.

23 Zan kashe ‘ya’yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.

24 Amma a game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da waɗansu suke kira zurfafan al’amuran Shaiɗan ba, ina ce muku, ban ɗora muku wani nauyi ba.

25 Sai dai ku riƙi abin da kuke da shi kankan, har in zo.

26 Duk wanda ya ci nasara, yake kuma kiyaye aikina har ƙarshe, shi zan bai wa iko a kan al’ummai,

27 zai kuwa mallake su da sanda ta ƙarfe, ya farfashe su kamar tukwanen yumɓu

28 (kamar yadda Ni ma kaina na sami iko a gun Ubana), zan kuma ba shi gamzaki.

29 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”