W. YAH 22

1 Sa’an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago,

2 ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar ‘ya’ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al’ummai ne.

3 Ba sauran wani abin la’antarwa, amma kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago, zai kasance a cikinsa. Bayinsa za su bauta masa,

4 za su kuma ga fuskarsa, sunansa kuwa zai kasance a goshinsu.

5 Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni’imar Mulki har abada abadin.

Yesu Yana Zuwa da Wuri

6 Sai ya ce mini, “Wannan magana tabbatacciya ce, ta gaskiya ce kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa ya aiko mala’ikansa, ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba.”

7 “Ga shi kuwa, ina zuwa da wuri. Albarka tā tabbata ga wanda yake kiyaye maganar annabcin littafin nan.”

8 Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa’ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala’ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.

9 Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ‘yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”

10 Ya kuma ce mini, “Kada ka rufe maganar annabcin littafin nan, domin lokaci ya kusa.

11 Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”

12 “Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi.

13 Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne na Ƙarshe.”

14 Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, domin su sami izinin ɗiba daga itacen rai, su kuma shiga birnin ta ƙofa.

15 Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.

16 “Ni Yesu, na aiko mala’ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”

17 Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

18 Ina yi wa duk mai jin maganar annabcin littafin nan kashedi, in wani ya yi wani ƙari a kanta, Allah zai ƙara masa bala’in da aka rubuta a littafin nan.

19 In kuma wani ya yi ragi a maganar littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai, da na tsattsarkan birnin, waɗanda aka rubuta a littafin nan.

20 Shi wanda ya shaida abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin! Zo, ya Ubangiji Yesu.

21 Alherin Ubangiji Yesu yă tabbata ga dukkan tsarkaka. Amin!