W. YAH 4

Sujada a Samaniya

1 Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”

2 Nan da nan kuwa Ruhu ya iza ni, sai ga wani kursiyi a girke a Sama, da wani a zaune a kai.

3 Na zaunen kuwa ya yi kama da yasfa da yakutu. Kewaye da kursiyin kuma akwai wani bakan gizo mai kama da zumurrudu.

4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.

5 Sai walƙiya take ta fitowa daga kursiyin, da ƙararraki, da kuma aradu. A gaban kursiyin kuma fitilu bakwai suna ci, waɗanda suke Ruhohin nan na Allah guda bakwai.

6 A gaban kursiyin kuwa akwai wani abu kamar bahar na gilas, garau yake kamar ƙarau.

Kewaye da kursiyin kuma, ta kowane gefensa, da waɗansu rayayyun halitta guda huɗu, masu idanu ta ko’ina, gaba da baya.

7 Rayayyiyar halittar farko kamar zaki take, ta biyu kuma kamar ɗan maraƙi, ta uku kuma da fuska kamar ta mutum, ta huɗu kuma kamar juhurma yana jewa.

8 Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa,

“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki,

Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”

9 Duk lokaci kuma da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wanda yake zaune a kan kursiyin, yake kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa,

10 sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,

11 “Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu,

Kă sami ɗaukaka, da girma, da iko,

Domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa,

Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”