YAK 5

Faɗaka ga Masu Arziki

1 To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙin ciki iri iri da za su aukar muku.

2 Arzikinku mushe ne! Tufafinku kuma duk cin asu ne!

3 Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan!

4 Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.

5 Kun yi zaman duniya da annashuwa da almubazzaranci, ashe, kiwata kanku kuka yi saboda ranar yanka!

6 Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.

Haƙuri da Addu’a

7 Domin haka, sai ku yi haƙuri, ‘yan’uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.

8 Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, domin ranar komowar Ubangiji ta yi kusa.

9 ‘Yan’uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari’a a bakin ƙofa!

10 A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, ‘yan’uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji.

11 Ga shi, mukan yaba wa waɗanda suka jure. Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarshen da Ubangiji ya yi masa, yadda Ubangiji yake mai yawan tausayi, mai jinƙai kuma.

12 Amma fiye da kome, ‘yan’uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A’a”, ya tsaya a kan “A’a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.

13 In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu’a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah.

14 In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji.

15 Addu’ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.

16 Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu’a, don a warkar da ku. Addu’ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.

17 Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu’a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba.

18 Da ya sāke yin addu’a kuwa, sai sama ta sako ruwa, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

19 Ya ku ‘yan’uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi,

20 to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi a hanya daga bauɗewarsa, ya kuɓutar da ran mai zunubin nan ke nan daga mutuwa, ya kuma rufe ɗumbun zunubansa.