YUSH 11

Ƙaunar Allah zuwa ga Mutanensa Masu Tayarwa

1 “A lokacin da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi,

Daga cikin Masar na kirawo ɗana.

2 Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini,

Sai ƙara miƙa wa Ba’al sadaka suke yi,

Suna ƙona turare ga gumaka.

3 Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya.

Na ɗauke su a hannuna,

Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.

4 Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna,

Na zama musu kamar wanda yake ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu.

Na sunkuya, na ciyar da su.

5 “Ba su koma ƙasar Masar ba,

Amma Assuriya za ta zama sarkinsu

Gama sun ƙi yarda su koma wurina.

6 Takobi zai ragargaje biranensu,

Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu,

Zai cinye su domin muguwar shawararsu.

7 Mutanena sun himmantu su rabu da ni,

Ko da yake an kira su ga Ubangiji,

Ba wanda ya girmama shi.

8 “Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu?

Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra’ila?

Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma?

Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim?

Zuciyata tana motsawa a cikina,

Juyayina ya huru.

9 Ba zan aikata fushina mai zafi ba,

Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba,

Gama ni Allah ne, ba mutum ba,

Maitsarki wanda yake tsakiyarku,

Ba zan zo wurinku da hasala ba.

10 “Za su bi Ubangiji,

Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri

‘Ya’yansa za su zo da rawar jiki da yamma.

11 Da sauri za su zo kamar tsuntsaye daga Masar,

Kamar kurciyoyi daga ƙasar Assuriya,

Zan komar da su gidajensu, ni Ubangiji na faɗa.”

An Tsauta wa Ifraimu domin Ƙarya da Zalunci

12 Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi,

Jama’ar Isra’ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta,

Yahuza kuma ta tayar wa Allah,

Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.