YUSH 4

Ubangiji Ya Soki Mutanen Isra’ila

1 Ya ku mutanen Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji,

Gama Ubangiji yana da shari’a da ku, ku mazaunan ƙasar.

“Gama ba gaskiya, ko ƙauna,

Ko sanin Ubangiji a ƙasar.

2 Akwai rantsuwa, da ƙarya, da kisankai, da sata, da zina,

Da kama-karya, da zub da jini a kai a kai.

3 Saboda haka ƙasar za ta yi makoki,

Dukan waɗanda yake zaune a cikinta za su yi yaushi.

Namomin jeji kuma, da tsuntsaye, da kifaye za su ƙare.

4 “Duk da haka kada wani ya sa wa mutum laifi,

Kada wani kuma ya tsautar.

Da ku nake magana, ku firistoci.

5 Za ku yi tuntuɓe da rana,

Annabi kuma zai yi tuntuɓe tare da kai da dare,

Ni kuwa zan hallaka mahaifiyarku.

6 Mutanena sun lalace saboda jahilci.

Tun da yake sun ƙi ilimi,

Ni ma na ƙi ku da zaman firist ɗina.

Tun da yake kun manta da umarnan Allahnka,

Ni ma zan manta da ‘ya’yanku.

7 “Yawan ƙaruwar firistoci, yawan ƙaruwar zunubi.

Zan sāke darajarsu ta zama kunya.

8 Suna ciyar da kansu da zunubin mutanena,

Suna haɗamar ribar muguntarsu.

9 Kamar yadda mutane suke, haka firistocin suke,

Zan hukunta su saboda al’amuransu,

Zan sāka musu gwargwadon ayyukansu.

10 Za su ci, amma ba za su ƙoshi ba.

Za su yi karuwanci, amma ba za su ƙaru ba.

Gama sun rabu da Ubangiji don su bauta wa gumaka.

11 “Karuwanci, da ruwan inabi,

Da ruwan inabin da bai sa hauka ba sukan kawar da hankali.

12 Mutanena sukan yi tambaya a wurin abin da aka yi da itace,

Sandansu yakan faɗa musu gaiɓu,

Gama ruhun karuwanci ya ɓad da su,

Sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci.

13 Suna miƙa sadaka a bisa ƙwanƙolin duwatsu.

Suna yin hadaya a bisa tuddai,

Da kuma a gindin itacen oak, da aduruku, da katambiri,

Domin suna da inuwa mai kyau.

Don haka ‘ya’yanku mata suke karuwanci,

Surukanku mata suke yin zina.

14 Ba zan hukunta ‘ya’yanku mata sa’ad da suka yi karuwanci ba,

Ko kuwa surukanku mata sa’ad da suka yi zina ba,

Gama mazan da kansu sukan shiga wurin karuwai.

Sukan miƙa sadaka tare da karuwai a Haikali,

Mutane marasa fahimi za su lalace.

15 “Ko da yake mutanen Isra’ila suna karuwanci,

Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi.

Kada ku tafi Gilgal,

Ko ku haura zuwa Bet-awen.

Kada ku yi rantsuwa da cewa,

‘Har da zatin Ubangiji!’

16 Mutanen Isra’ila masu taurinkai ne kamar alfadari.

Ta yaya Ubangiji zai yi kiwonsu

Kamar ‘ya’yan tumaki a makiyaya mai fāɗi?

17 Mutanen Ifraimu sun haɗa kai da gumaka,

Sai a rabu da su.

18 Su taron mashaya ne kawai,

Karuwai ne kuma.

Suna ƙaunar abin kunya.

19 Iska ta ƙunshe su cikin fikafikanta.

Za su ji kunyar bagadansu.”