YUSH 9

Hukuncin da Za A Yi wa Isra’ila domin Rashin Aminci

1 Kada ku yi farin cikin, ya mutanen Isra’ila!

Kada ku yi murna kamar sauran mutane!

Gama kun yi karuwanci, kun rabu da Allahnku.

Kuna ƙaunar ijarar karuwanci a kowane masussuka.

2 Masussuka da wurin matsa ruwan inabi ba za su ciyar da su ba.

Sabon ruwan inabi kuma ba zai ishe su ba.

3 Ba za su zauna a ƙasar Ubangiji ba,

Amma mutanen Ifraimu za su koma Masar.

Za su ci haramtaccen abinci a Assuriya.

4 Ba za su yi wa Ubangiji hadaya ta sha ba.

Ba za su faranta zuciyarsa da sadakoki ba.

Abincinsu zai zama irin na masu makoki.

Duk wanda ya ci shi zai haramta.

Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai,

Ba za su kai shi Haikalin Ubangiji ba.

5 Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar idi?

Da a ranar idin Ubangiji?

6 Ga shi kuma, suna tafiya zuwa halaka,

Masar za ta tattara su,

Memfis za ta binne su.

Ƙayayuwa za su mallaki abubuwan tamaninsu na azurfa.

Sarƙaƙƙiya za ta tsiro a cikin alfarwansu.

7 Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso,

Isra’ila za ta sani!

An ce annabi wawa ne,

Mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne,

Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.

8 Ifraimu mai tsaro ne a gaban Allahna, annabi kuwa,

Duk da haka sun zama kamar mai kafa tarkon kama tsuntsu, a farkon kaka.

Akwai ƙiyayya a cikin Haikalin Allahnsu.

9 Sun yi zurfi cikin rashin gaskiya

Kamar a kwanakin Gibeya,

Ubangiji zai tuna da muguntarsu.

Zai hukunta su saboda zunubansu.

10 Ubangiji ya ce, “Na iske Isra’ila a jeji kamar inabi,

Na ga kakanninku kamar nunan fari na ‘ya’yan ɓaure,

Amma da suka zo Ba’al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba’al.

Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.

11 Darajar Ifraimu za ta tashi kamar tsuntsu,

Ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki!

12 Ko sun goyi ‘ya’ya,

Zan sa su mutu tun ba su balaga ba.

Tasu ta ƙare sa’ad da na rabu da su!”

13 Ya Ubangiji, na ga yadda Ifraimu

Ta mai da ‘ya’yanta ganima

Tana fitar da su zuwa wurin yanka.

14 Ya Ubangiji, me zan ce ka ba su?

Me za ka ba su?

Ka ba su cikin da ba ya haihuwa da busassun mama.

15 Ubangiji ya ce, “Kowace irin muguntarsu tana a Gilgal,

A can na ƙi su!

Saboda mugayen ayyukansu, zan kore su daga ƙasata,

Ba kuma zan ƙaunace su ba.

Dukan shugabanninsu ‘yan tayarwa ne.

16 An ka da mutanen Ifraimu, saiwarsu ta bushe.

Ba za su yi ‘ya’ya ba.

Ko ma sun haihu, zan kashe ‘ya’yan nan nasu waɗanda suke ƙauna.”

17 Allahna zai ƙi su

Domin ba su yi masa biyayya ba.

Za su zama masu yawo cikin al’ummai.