ZAB 103

Yabon Ƙaunar Allah

1 Ka yabi Ubangiji, ya raina!

Ka yabi sunansa mai tsarki!

2 Ka yabi Ubangiji, ya raina,

Kada ka manta da yawan alherinsa.

3 Ya gafarta dukan zunubaina,

Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.

4 Ya cece ni daga kabari,

Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.

5 Ya cika raina da kyawawan abubuwa,

Don in zauna gagau,

Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.

6 Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari’a ta gaskiya.

Yakan ba su hakkinsu.

7 Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa.

Ya yardar wa jama’ar Isra’ila su ga manyan ayyukansa.

8 Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma,

Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.

9 Ba zai yi ta tsautawa kullum ba,

Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.

10 Yakan yi mana rangwame sa’ad da yake hukunta mu,

Ko sa’ad da yake sāka mana saboda zunubanmu da laifofinmu.

11 Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya,

Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.

12 Kamar yadda gabas take nesa da yamma,

Haka nan ne ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.

13 Kamar yadda uba yake yi wa ‘ya’yansa alheri,

Haka nan kuwa Ubangiji yake yi wa masu tsoronsa alheri.

14 Ubangiji ya san abin da aka yi mu da shi,

Yakan tuna, da ƙura aka yi mu.

15 Mutum fa, ransa kamar ciyawa ne,

Yakan yi girma, ya yi yabanya kamar furen jeji.

16 Sa’an nan iska ta bi ta kansa, yakan ɓace,

Ba mai ƙara ganinsa.

17 Amma ƙaunar Ubangiji ga waɗanda suke girmama shi har abada ce.

Alherinsa kuwa tabbatacce ne har dukan zamanai,

18 Ga waɗanda suke riƙe da alkawarinsa da gaskiya,

Waɗanda suke biyayya da umarnansa da aminci.

19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama,

Shi yake sarautar duka.

20 Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala’iku,

Ku da kuke biyayya da umarnansa,

Kuna kasa kunne ga maganarsa!

21 Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da suke a Sama,

Ku yabi Ubangiji, ku bayinsa masu aikata abin da yake so!

22 Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa,

A duk inda yake mulki!

Ka yabi Ubangiji, ya raina!