ZAB 145

Waƙar Yabon Allah domin Alherinsa da Ikonsa

1 Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina,

Zan yi maka godiya har abada abadin.

2 Kowace rana zan yi maka godiya,

Zan yabe ka har abada abadin.

3 Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa,

Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.

4 Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara,

Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.

5 Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka,

Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

6 Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka,

Ni kuwa zan yi shelar girmanka.

7 Za su ba da labarin girmanka duka,

Su kuma raira waƙa a kan alherinka.

8 Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi,

Cike da madawwamiyar ƙauna.

9 Shi mai alheri ne ga kowa,

Yana juyayin dukan abin da ya halitta.

10 Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka,

Jama’arka kuma za su yi maka godiya!

11 Za su yi maganar darajar mulkinka,

Su ba da labarin ikonka,

12 Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka,

Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.

13 Mulkinka, madawwamin mulki ne,

Sarki ne kai har abada.

14 Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala,

Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.

15 Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi,

Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,

16 Yana kuwa ba su isasshe,

Yakan biya bukatarsu duka.

17 Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka,

Mai jinƙai ne a ayyukansa duka.

18 Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi,

Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.

19 Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa,

Yakan ji kukansu, ya cece su.

20 Yakan kiyaye dukan waɗanda suke ƙaunarsa,

Amma zai hallaka mugaye duka.

21 A kullum zan yabi Ubangiji,

Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada!