ZAB 70

Addu’ar Neman Kuɓuta

1 Ka cece ni, ya Allah!

Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!

2 Ka sa masu so su kashe ni,

A ci nasara a kansu, su ruɗe!

Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya!

3 Ka sa waɗanda suke mini ba’a

Su razana sabili da fāɗuwarsu!

4 Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka

Su yi murna, su yi farin ciki!

Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka

Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”

5 Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,

Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.

Kai ne mataimakina da Mai Cetona,

Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!