ZAB 78

Amincin Allah ga Jama’arsa

1 Ku kasa kunne ga koyarwata, ya ku jama’ata,

Ku kula da abin da nake faɗa.

2 Zan yi magana da ku,

In faɗa muku asirai na dā,

3 Abubuwan da muka ji muka kuwa sani,

Waɗanda kakanninmu suka faɗa mana.

4 Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga ‘ya’yanmu ba,

Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwa

Labarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa,

Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.

5 Ya ba da dokoki ga jama’ar Isra’ila,

Da umarnai ga zuriyar Yakubu.

Ya ba kakanninmu ka’idodi,

Don su koya wa ‘ya’yansu dokokinsa,

6 Saboda tsara mai zuwa ta koye su,

Su kuma su koya wa ‘ya’yansu.

7 Ta haka su ma za su dogara ga Allah,

Ba za su manta da abin da ya yi ba,

Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.

8 Kada su zama kamar kakanninsu,

Jama’ar ‘yan tawaye marasa biyayya.

Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba,

Ba su kuwa yi masa aminci ba.

9 Ifraimawa waɗanda suka yi yaƙi da bakkuna da kibau

Suka gudu a ranar yaƙi.

10 Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba,

Sun ƙi biyayya da dokokinsa.

11 Sun manta da abin da ya aikata,

Da mu’ujizan nan da ya nuna musu.

12 Kakanninsu na kallo sa’ad da Allah ya aikata wata mu’ujiza

A filin Zowan a ƙasar Masar.

13 Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta,

Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.

14 Da rana sai ya bi da su da girgije,

Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.

15 Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada,

Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.

16 Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse,

Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.

17 Amma sun ci gaba da yi wa Allah zunubi,

A hamada suka yi wa Maɗaukaki tawaye.

18 Da gangan suka jarraba Allah,

Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.

19 Suka yi magana gāba da Allah, suka ce,

“Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?

20 Gaskiya ce, ya bugi dutse,

Ruwa kuwa ya fito a yalwace,

Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama’arsa?”

21 Saboda haka Allah ya yi fushi sa’ad da ya ji su,

Ya aukar wa jama’arsa da wuta,

Fushinsa ya haɓaka a kansu,

22 Saboda ba su amince da shi ba,

Ba su kuma gaskata yana da ikon cetonsu ba.

23 Amma ya yi magana da sararin sama,

Ya umarci ƙofofinsa su buɗe,

24 Ya ba su tsaba daga sama,

Da ya sauko musu da manna, su ci.

25 Ta haka suka ci abincin mala’iku.

Allah ya ba su iyakar abin da za su iya ci.

26 Sa’an nan sai ya sa iskar gabas ta hura,

Da ikonsa kuma ya sa iskar kudu ta tashi.

27 Ya aika da tsuntsaye bisansu kamar ƙura,

Yawansu kamar yashi a gaɓa,

28 Sai suka fāɗo a zango,

Kewaye da alfarwai ko’ina.

29 Sai mutane suka ci suka ƙoshi,

Allah ya ba su iyakar abin da suke bukata.

30 Amma sa’ad da suke cikin ci,

Tun ba su ƙoshi ba,

31 Sai Allah ya yi fushi da su.

Ya karkashe ƙarfafan mutane,

Da samarin Isra’ila na gaske!

32 Ko da yake ya aikata mu’ujizai da yawa,

Duk da haka jama’a suka ci gaba da yin zunubi,

Ba su kuwa gaskata shi ba.

33 Ta haka ya ƙare kwanakinsu kamar fitar numfashi,

Bala’i ya aukar wa rayukansu farat ɗaya.

34 Amma sa’ad da ya kashe waɗansunsu,

Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba,

Suka yi addu’a sosai a gare shi.

35 Sun tuna, ashe, Allah ne mai kiyaye su,

Sun tuna Maɗaukaki shi ne Mai Fansarsu.

36 Amma maganganunsu duka ƙarya ne,

Dukan abin da suka faɗa kuwa daɗin baki ne kawai.

37 Ba su yi masa biyayya ba,

Ba su yi aminci game da alkawarin da suka yi da shi ba.

38 Amma Allah ya yi wa jama’arsa jinƙai,

Ya gafarta zunubansu,

Bai hallaka su ba.

Sau da yawa yakan kanne fushinsa,

Ya dakatar da hasalarsa.

39 Yakan tuna su mutane ne kawai,

Kamar iskar da take hurawa ta wuce .

40 Sau da yawa suka tayar masa a hamada.

Sau da yawa suka sa shi yin ɓacin rai!

41 Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai,

Suka kuwa sa Mai Tsarki na Isra’ila yin fushi.

42 Suka manta da ikonsa mai girma.

Suka manta da lokacin da ya cece su daga abokan gābansu,

43 Lokacin da ya aikata manyan ayyuka da mu’ujizai

A filin Zowan, ta ƙasar Masar.

44 Ya mai da koguna su zama jini,

Masarawa kuwa suka kasa sha daga rafuffukansu.

45 Ya aiko da ƙudaje gare su, suka wahalshe su,

Kwaɗi suka lalata filayensu.

46 Ya aiko da gamzari don su ci amfanin gonakinsu,

Ya aiko da ɗango su lalata gonakinsu.

47 Ya kashe kurangar inabinsu da ƙanƙara,

Ya kuma kashe itatuwan ɓaurensu da jaura.

48 Ya karkashe shanunsu da ƙanƙara,

Ya kuma karkashe garkunan tumakinsu da na awakinsu da tsawa.

49 Ya buge su da fushinsa mai zafi, da hasalarsa,

Ya sa su damuwa ƙwarai,

Da ya aiko da mala’iku masu hallakarwa.

50 Bai kanne fushinsa ba,

Bai bar su da rai ba,

Amma ya karkashe su da annoba.

51 Ya karkashe ‘yan fari maza

Na dukan iyalan da suke Masar.

52 Sa’an nan ya bi da jama’arsa

Kamar makiyayi, ya fito da su,

Ya yi musu jagora cikin hamada.

53 Ya bi da su lafiya, ba su kuwa ji tsoro ba,

Amma teku ta cinye abokan gābansu.

54 Ya kawo su tsattsarkar ƙasarsa,

Ya kawo su a duwatsun da shi kansa ya ci da yaƙi.

55 Ya kori mazaunan wurin sa’ad da jama’arsa suka dirkako,

Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra’ila,

A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.

56 Amma sai suka yi wa Allah Mai Iko Dukka tawaye,

Suka jarraba shi.

Ba su kiyaye dokokinsa ba,

57 Amma suka yi tawaye da rashin aminci

Kamar kakanninsu,

Kamar kiban da aka harba da tanƙwararren baka,

Waɗanda ba su da tabbas.

58 Suka sa shi ya yi fushi saboda

Masujadansu na arnanci.

Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.

59 Allah ya yi fushi sa’ad da ya ga haka,

Don haka ya rabu da jama’arsa ɗungum.

60 Ya bar alfarwarsa da take a Shilo,

Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.

61 Ya yardar wa abokan gāba su ƙwace akwatin alkawari,

Inda aka ga ikonsa da darajarsa,

62 Ya ji fushi da jama’arsa,

Ya bar abokan gābansu su karkashe su.

63 Aka karkashe samari a cikin yaƙi,

‘Yan mata kuma suka rasa ma’aura.

64 Aka karkashe firistoci da takuba,

Matansu ba su yi makoki dominsu ba.

65 Daga bisani sai Ubangiji ya tashi

Kamar wanda ya farka daga barci,

Kamar jarumi wanda ya bugu da ruwan inabi.

66 Ya tura abokan gābansa baya,

Da mummunar kora mai bankunya

Da ba za su sāke tashi ba.

67 Ubangiji ya rabu da zuriyar Yusufu,

Bai kuma zaɓi kabilar Ifraimu ba.

68 A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza.

Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.

69 A can ya gina Haikalinsa,

Kamar wurin zamansa a Sama.

Ya kafa shi da ƙarfi kamar duniya,

Tabbatacce a kowane lokaci.

70 Ya zaɓi bawansa Dawuda,

Ya ɗauko shi daga wurin kiwon tumaki,

71 Ya ɗauko shi daga inda yake lura da ‘yan raguna.

Ya naɗa shi Sarkin Isra’ila,

Ya naɗa shi makiyayin jama’ar Allah.

72 Dawuda kuwa ya lura da su da zuciya ɗaya,

Da gwaninta kuma ya bi da su.