ZAB 90

Allah Madawwami, Mutum mai Shuɗewa

1 Ya Ubangiji, a koyaushe kai ne wurin zamanmu.

2 Kafin a kafa tuddai,

Kafin kuma ka sa duniya ta kasance,

Kai Allah ne, Madawwami.

Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.

3 Kakan sa mutane su koma yadda suke,

Su zama ƙura.

4 A gare ka shekara dubu, kamar kwana ɗaya ne,

Kamar jiya ce wadda ta shige,

Gajeruwa ce kamar sa’a guda ta dare.

5 Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi,

Kamar mafarki suke, ba su daɗewa.

Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,

6 Su yi girma har su yi huda,

Sa’an nan su yi yaushi su bushe da yamma.

7 Mun halaka ta wurin fushinka,

Mun razana saboda hasalarka.

8 Ka jera zunubanmu a gabanka,

Zunubanmu na ɓoye kuwa,

Ka sa su a inda za ka gan su.

9 Fushinka ya gajerta tsawon ranmu,

Ranmu ya ƙare kamar ajiyar zuciya.

10 Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba’in,

In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne.

Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru

Suke kawo mana, damuwa ce da wahala,

Nan da nan sukan wuce,

Tamu da ƙare.

11 Wa ya san iyakar ikon fushinka?

Wa ya san irin tsoron da hasalarka za ta kawo?

12 Ka koya mana mu sani ranmu na ɗan lokaci ne,

Domin mu zama masu hikima.

13 Ya Ubangiji, sai yaushe za ka ji tausayinmu?

Ka ji tausayin bayinka!

14 Ka cika mu da madawwamiyar ƙaunarka a kowace safiya,

Don mu raira waƙoƙin murna dukan kwanakin ranmu.

15 Yanzu sai ka sa mu yi farin ciki mai yawa,

Kamar yadda ka sa muka yi baƙin ciki

A dukan shekarun nan, da muka sha wahala.

16 Ka yarda mana, mu bayinka, mu ga ayyukanka masu girma,

Ka yardar wa zuriyarmu su ga ikonka mai girma.

17 Ka yarda, albarkarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu.

Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi!

I, ka ba mu nasara a dukan abin da muke yi!