Allah Sarki Ne
1 Ubangiji sarki ne!
Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne.
Hakika duniya ta kahu sosai a inda take,
Ba kuwa za ta jijjigu ba.
2 Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko,
Kana nan tun fil azal.
3 Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu,
Suna ta da muryarsu da ruri.
4 Ubangiji yana mulki cikin Sama,
Mulkinsa mafifici ne,
Fiye da rurin teku,
Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.
5 Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji,
Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai,
Har abada abadin.