ZAF 2

Za a Hallaka Al’umman da Suke Kewaye da Su

1 Ya ke al’umma marar kunya, ku tattaru, ku yi taro,

2 Kafin a zartar da umarni,

Kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi,

Kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku,

Kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku.

3 Ku nemi Ubangiji,

Dukanku masu tawali’u na duniya,

Ku waɗanda kuke bin umarninsa.

Ku nemi adalci da tawali’u.

Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.

4 Za a bar Gaza ba kowa,

Ashkelon za ta zama kufai,

Za a kori mutanen Ashdod da tsakar rana,

Ekron kuwa za a tumɓuke ta.

5 Taku ta ƙare, ku mazaunan gaɓar teku, ke al’ummar Keretiyawa!

Ya Kan’ana, ƙasar Filistiyawa,

Maganar Ubangiji tana gāba da ke,

Za a hallaka ki har ba wanda zai ragu.

6 Gāɓar teku za ta zama makiyaya, da wurin zaman masu kiwo,

Da kuma garakan tumaki.

7 Gaɓar teku za ta zama ta mutanen Yahuza waɗanda suka ragu,

Wurin da za su yi kiwo.

Za su kwanta da maraice a gidajen Ashkelon,

Gama Ubangiji Allahnsu zai kula da su,

Zai kuwa mayar musu da albarkarsu ta dā.

8 “Na ji ba’ar da Mowab ta yi, da zagin Ammonawa,

Yadda suka yi wa mutanena ba’a,

Sun yi alwashi, cewa za su cinye ƙasarsu.

9 Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra’ila,

Na rantse cewa,

Mowab za ta zama kamar Saduma,

Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata.

Za su zama ƙasar ƙayayuwa

Da kwazazzaban gishiri marar amfani har abada.

Mutanena waɗanda suka ragu za su washe su, su mallake su.”

10 Wannan shi ne hakkin girmankansu,

Saboda sun raina jama’ar Ubangiji Mai Runduna,

Sun yi musu alfarma.

11 Ubangiji zai tsananta musu,

Zai kawo wa dukan gumakan da yake a duniya yunwa.

Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake,

Har da ƙasar sauran al’umma.

12 “Ku kuma, Habashawa, za a kashe ku da takobina.”

13 Zai miƙa hannunsa gāba da arewa,

Zai hallaka Assuriya,

Zai mai da Nineba busasshen kufai

Marar amfani kamar hamada.

14 Tumaki za su kwanta a tsakiyarta,

Da kuma kowace irin dabba ta kowace ƙasa.

Mujiya da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta,

Ga muryar kuka a taga.

Ga risɓewa a bakin ƙofa,

Gama za a kware rufin katakan itacen al’ul.

15 Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya,

Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.”

Ga shi, ya zama kufai,

Wurin zaman dabbobi!

Duk wanda ya wuce ta wurin,

Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.