ZAK 1

Ubangiji Ya Kira Mutanensa Su Komo gare Shi

1 A watan takwas a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo, ya ce,

2 “Ubangiji ya yi fushi da kakanninku.

3 Domin haka sai ka ce musu, Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ku komo wurina, ni kuma zan komo wurinku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’

4 Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa.

5 To, ina kakannin nan naku suke? Annabawan fa? Suna da rai har wa yau?

6 Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”

Wahayin Dawakai da Zakariya Ya Gani

7 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya kuma yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo.

8 Da dare, na ga mutum yana kan aharashin doki, yana tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙi, a kwari. A bayansa kuma ga wani aharashin doki, da bidi, da kili.

9 Sai na ce, “Mene ne waɗannan, ya Ubangiji?”

Mala’ikan da ya yi magana da ni ya ce, “Zan bayyana maka ma’anarsu.”

10 Sai mutumin da yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne Ubangiji ya aike su su yi tsaron duniya, suna kai da kawowa.”

11 Sai suka ce wa mala’ikan Ubangiji wanda yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun yi ta kai da kawowa a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”

12 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, har yaushe za ka ƙi nuna jinƙai ga Urushalima da biranen Yahuza, waɗanda kake jin haushinsu shekara saba’in ke nan?”

13 Sai Ubangiji ya amsa wa mala’ikan da yake magana da ni da magana ta alheri da ta ta’azantarwa.

14 Mala’ikan kuma da yake magana da ni ya ce, in yi shela in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce yana jin ƙishin Urushalima da Sihiyona ƙwarai.

15 Yana fushi ƙwarai da al’umman duniya da take zaman lafiya, gama ya yi ɗan fushi da mutanena, amma su suka yi musu hukuncin da ya zarce.

16 Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma’auni.”

17 Ya ce, in kuma yi shela, in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce wadata za ta sake bunƙasa cikin biranensa, zai kuma ta’azantar da Sihiyona, ya kuma zaɓi Urushalima.”

Wahayin Ƙahoni da Maƙera da Zakariya Ya Gani

18 Da na ɗaga idona, sai na ga ƙahoni huɗu.

19 Sai na ce wa mala’ikan da ya yi magana da ni, “Mene ne waɗannan?”

Shi kuwa ya ce mini, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza, da Isra’ila, da Urushalima.”

20 Sa’an nan kuma Ubangiji ya nuna mini waɗansu maƙera, su huɗu.

21 Sai na ce, “Me waɗannan suke zuwa su yi?”

Sai ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza don kada mutum ya ɗaga kansa. Waɗannan kuwa sun zo don su tsorata su, su karya ƙahonin al’umman duniya waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuza don su warwatsa ta.”