ZAK 12

Za a Ceci Urushalima nan Gaba

1 Ga maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji wanda ya shimfiɗa sammai, ya kirkiro duniya, ya kuma sa rai a cikin mutum, ya ce,

2 “Ga shi, ina gab da sa Urushalima ta zama ƙoƙon sa tangaɗi ga dukan al’ummai da yake kewaye. Yaƙin da zai kewaye Urushalima zai shafi Yahuza ita ma.

3 A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al’ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al’umman duniya za su taru su kewaye ta.

4 A wannan rana zan firgita kowane doki, in sa mahayinsa ya haukace. Zan lura da mutanen Yahuza, amma zan makantar da dawakan abokan gābansu.

5 Sa’an nan iyalan Yahuza za su ce wa kansu, ‘Ubangiji Allah Maɗaukaki yana ƙarfafa mutanensa waɗanda suke zaune a Urushalima.’

6 “A ranan nan zan sa iyalan Yahuza su zama kamar wuta a kurmi, ko kuwa a gonar da hatsi ya nuna. Za su halaka dukan al’umman da suke kewaye da su. Amma mutanen Urushalima za su yi zamansu lami lafiya.

7 “Ubangiji zai fara ba mutanen Yahuza nasara, domin kada darajar jama’ar Dawuda da ta mazaunan Urushalima ta fi ta mutanen Yahuza.

8 A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama’ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji a gabansu.

9 A ranar kuma zan hallaka dukan al’umman da suka zo su yi yaƙi da Urushalima.

10 “Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu’a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.

11 A ran nan za a yi babban makoki a Urushalima kamar mutane suka yi wa Hadadrimmon a filin Magiddo.

12 Kowane iyali a ƙasar za su yi makokinsu a keɓe, iyalin gidan Dawuda kuma za su yi nasu a keɓe, matansu za su yi nasu a keɓe. Iyalin gidan Natan su ma za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.

13 Iyalin gidan Lawi za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe. Iyalin gidan mutanen Shimai za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe.

14 Sauran dukan iyalan da suka ragu za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.”