ZAK 3

Wahayin Yoshuwa Babban Firist da Zakariya Ya Gani

1 Ubangiji ya nuna mini Yoshuwa, babban firist, yana tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji. Shaiɗan kuma yana tsaye dama da mala’ikan, yana saran Yoshuwa.

2 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsauta maka, kai Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima ya tsauta maka. Ai, wannan mutum kamar itace ne wanda aka fizge daga cikin wuta.”

3 Yoshuwa dai yana tsaye a gaban mala’ikan saye da riguna masu dauɗa.

4 Mala’ikan kuwa ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku tuɓe masa rigunan nan masu dauɗa.” Sa’an nan ya ce wa Yoshuwa, “Ga shi, na kawar maka da laifinka, zan sa maka riguna masu daraja.”

5 Sai ni kuma na ce, “Bari kuma su naɗa masa rawani mai tsabta.” Suka kuwa naɗa masa rawani mai tsabta, suka kuma sa masa riguna sa’ad da mala’ikan Ubangiji yana nan a tsaye.

6 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya gargaɗi Yoshuwa, ya ce,

7 “Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.

8 Ka ji, ya Yoshuwa, babban firist, kai da abokanka da suke zaune gabanka, ku alama ce mai kyau. Ga shi, zan kawo bawana mai suna Reshe.

9 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a kan dutsen da na kafa a gaban Yoshuwa, dutse mai ido bakwai zan yi rubutu, zan kawar da laifin al’umman nan rana ɗaya.

10 A wannan rana kowane ɗayanku zai gayyaci maƙwabcinsa zuwa gindin kurangar inabinsa da itacen ɓaurensa.’ ”