ZAK 5

Wahayin Littafi na Tashi Sama

1 Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama.

2 Sai mala’ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”

Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”

3 Sa’an nan ya ce mini, “Wannan la’ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya.

4 Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”

Wahayin Mace a cikin Kwando

5 Sa’an nan mala’ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”

6 Ni kuwa na ce masa, “Mene ne wannan?”

Ya ce, “Wannan babban kwando ne wanda ya fita.” Ya kuma ce, “Wannan mugunta ce a dukan ƙasar.”

7 Da aka ɗaga murfin kwando na darma, sai ga mace tana zaune a cikin kwandon!

8 Sai ya ce, “Wannan mugunta ce.” Sa’an nan ya tura ta cikin kwandon, ya rufe bakin kwandon da murfi na darma mai nauyi.

9 Da na ɗaga idona, sai na ga mata biyu suna matsowa. Iska tana hura fikafikansu, gama suna da fikafikai kamar na shamuwa. Suka ɗaga kwandon sama.

10 Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni, na ce, “Ina za su kai kwandon?”

11 Ya ce mini, “Za su tafi da shi ƙasar Shinar don su gina masa haikali, sa’ad da suka gama ginin, za su ajiye shi a ciki.”