ZAK 9

Hukuncin da Za a Yi wa Al’umman da Suke Kewaye

1 Ubangiji ya yi magana gāba da ƙasar Hadrak, da kuma gāba da Dimashƙu. Ubangiji ne yake lura da ‘yan adam duk da kabilan Isra’ila.

2 Ubangiji kuma yana gāba da Hamat wadda yake kan iyaka, yana kuma gāba da Taya da Sidon ko da yake suna da hikima ƙwarai.

3 Taya ta gina wa kanta kagara,

Ta kuma tara azurfa kamar ƙura,

Zinariya kuma kamar sharar titi.

4 Amma Ubangiji zai washe ta,

Ya zubar da dukiyarta a cikin teku,

Wuta kuma za ta cinye ta.

5 Ubangiji ya ce,

“Ashkelon za ta gani ta ji tsoro,

Gaza kuma za ta yi makyarkyata da azaba,

Haka kuma Ekron za ta fid da zuciya,

Sarki zai halaka cikin Gaza,

Ashkelon za ta zama kufai.

6 Tattarmuka za su zauna a Ashdod,

Zan kuma sa alfarmar Filistiya ta ƙare.

7 Zan kawar da jininsu daga bakinsu,

Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu.

Sauransu za su zama jama’ar Allahnmu,

Za su zama kamar sarki cikin Yahuza.

Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.

8 Zan kafa sansani kewaye da Haikalina saboda maƙiya,

Don masu kai da kawowa.

Ba wani azzalumi da zai ci su da yaƙi,

Gama yanzu ni kaina na gani.”

Sarki Mai Zuwa

9 Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona!

Ta da murya ya Urushalima!

Ga Sarkinki yana zuwa wurinki,

Shi mai adalci ne, mai nasara,

Shi kuma mai tawali’u ne,

Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.

10 Ubangiji ya ce,

“Zan datse karusa daga Ifraimu,

In datse ingarman yaƙi a Urushalima,

Zan kuma karya bakan yaƙi.

Sarkinki zai tabbatar wa al’umman duniya da salama,

Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku,

Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”

Za a Rayar da Sihiyona

11 Ubangiji ya ce,

“Ke kuma, saboda jinin alkawarina da yake tsakanina da ke,

Zan ‘yantar da waɗanda suke cikin rami,

Waɗanda aka kama daga cikinki.

12 Ku koma mafakarku, ku ɗaurarru masu sa zuciya.

Gama yanzu zan sāka muku har ninki biyu.

13 Gama na tankwasa Yahuza ta zama bakana,

Na kuma mai da Ifraimu ta zama kibiya,

Zan yi amfani da mutanen Sihiyona kamar takobi,

Su yi yaƙi da mutanen Hellas.”

14 Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su,

Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya,

Ubangiji Allah zai busa ƙaho,

Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.

15 Ubangiji Mai Runduna zai tsare su,

Za su tattake duwatsun majajjawa,

Za su sha jini kamar ruwan inabi,

Za su cika kamar tasar ruwan inabi,

Kamar kuma kusurwoyin bagade.

16 A wannan rana Ubangiji Allahnsu zai cece su,

Gama su jama’arsa ne, garkensa kuma,

Kamar yadda lu’ulu’u yake haske a kambi,

Haka za su yi haske a ƙasarsa.

17 Wane irin kyau da bansha’awa alherinsa yake!

Hatsi zai sa samari su yi murna.

Sabon ruwan inabi kuma zai sa ‘yan mata su yi farin ciki.