Haihuwar Sama’ila
1 Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.
2 Yana da mata biyu, sunayensu Hannatu da Feninna. Feninna tana da ‘ya’ya, amma Hannatu ba ta haihuwa.
3 A kowace shekara Elkana yakan haura daga garinsu zuwa Shilo domin ya miƙa wa Ubangiji Mai Runduna hadaya, ya kuma yi masa sujada. ‘Ya’yan Eli, maza biyu, Hofni da Finehas, su ne firistoci na Ubangiji a can.
4 Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da ‘ya’yanta mata da maza nasu rabo.
5 Amma Hannatu, sai ya ba ta babban rabo guda ɗaya, gama yana ƙaunarta, amma Ubangiji ya kulle mahaifarta.
6 Kishiyarta takan tsokane ta don ta ji haushi, gama Ubangiji ya hana mata haihuwa.
7 Haka aka yi ta yi kowace shekara, duk lokacin da suka tafi domin yin sujada, sai Feninna ta tsokane ta. Don haka Hannatu ta yi ta kuka, ta ƙi cin abinci.
8 Elkana mijinta kuwa, ya ce mata, “Hannatu, me ya sa kike kuka? Me ya sa kike ƙin cin abinci? Me ya sa zuciyarki ta ɓaci? Ni ban fi ‘ya’ya maza goma a gare ki ba?”
Hannatu da Eli
9 Wata rana a Shilo bayan da sun gama cin abinci, sai Hannatu ta tashi. Eli, firist, kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar masujadar Ubangiji.
10 Hannatu tana fama da baƙin ciki ƙwarai, sai ta yi addu’a, tana kuka da ƙarfi ga Ubangiji.
11 Ta yi wa’adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”
12 Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa’ad da take yin addu’a.
13 Gama ta yi addu’ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,
14 ya kuwa ce mata, “Sai yaushe za ki daina maye? Ki daina shan ruwan inabi.”
15 Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.
16 Kada ka zaci ni ‘yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”
17 Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra’ila ya amsa miki roƙonki.”
18 Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa’an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.
Haihuwar Sama’ila da Miƙawarsa
19 Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa’an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.
20 Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama’ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”
21 Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa’adinsa.
22 Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.”
23 Elkana ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi kyau, ki jira har ki yaye shi, Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Hannatu ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta.
24 Sa’ad da ta yaye yaron, sai ta ɗauke shi, ta kuma ɗauki bijimi bana uku, da mudun gari, da salkar ruwan inabi, ta kai shi ɗakin Ubangiji a Shilo, yaron kuwa yana ɗan ƙarami.
25 Sai suka yanka bijimin, suka kuma kai yaron wurin Eli.
26 Sa’an nan Hannatu ta ce, “Gafara dai, ba ka tuna da ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana roƙon Ubangiji.
27 Na roƙi Ubangiji wannan yaro, Ubangiji kuwa ya biya mini bukatata da na roƙa a gare shi.
28 Saboda haka nake miƙa shi ga Ubangiji muddin ransa. Ya zama na Ubangiji.”
A can ya yi wa Ubangiji sujada.