RUT 4

Bo’aza ya Auri Rut

1 Bo’aza fa ya tafi, ya zauna a dandalin ƙofar gari. Sai ga wani daga cikin waɗanda hakkinsu ne su ɗauki Rut, shi ne kuwa wanda Bo’aza ya ambata, ya iso. Bo’aza kuwa ya ce masa, “Ratso nan, wāne, ka zauna.” Sai ya ratsa, ya zauna.

2 Bo’aza ya kuma kirawo goma daga cikin dattawan gari, ya ce musu, “Ku zauna nan.” Suka kuwa zauna.

3 Sa’an nan ya ce wa dangin nan nasa na kusa, “Ga Na’omi wadda ta komo daga ƙasar Mowab, tana so ta sayar da gonar Elimelek danginmu.

4 Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama’a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.”

Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”

5 Sa’an nan Bo’aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na’omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”

6 Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.”

7 Wannan ita ce al’adar Isra’ilawa a dā a kan sha’anin fansa ko musaya, don tabbatar da al’amarin. Sai mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen. Wannan ita ce hanyar tabbatarwa a cikin Isra’ila.

8 Saboda haka a sa’ad da dangin nan mafi kusa ya ce wa Bo’aza, “Sai ka saye ta,” sai ya tuɓe takalminsa ya ba Bo’aza.

9 Sa’an nan Bo’aza ya ce wa dattawan da dukan jama’ar da suke wurin, “Yau ku ne shaidu, cewa, na sayi dukan abin da yake na Elimelek, da na Kiliyon, da na Malon daga hannun Na’omi.

10 Game da wannan kuma Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayi Malon, ta zama matata domin in wanzar da sunan marigayin cikin gādonsa, don kada sunansa ya mutu daga na ‘yan’uwansa, da kuma a garinsu. Ku ne fa shaidu a yau.”

11 Dukan jama’a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai’atu waɗanda suka gina gidan Isra’ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,

12 gidanku kuma ya zama kamar gidan Feresa, wanda Tamar ta haifa wa Yahuza, saboda ‘ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace.”

13 Bo’aza kuwa ya auri Rut, ta zama matarsa. Ya kuma shiga wurinta, Ubangiji kuwa ya sa ta yi ciki, ta haifa masa ɗa.

14 Sai mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, da bai bar ki bā dangi na kusa ba, Allah ya sa ɗan ya yi suna a cikin Isra’ila.

15 Ya zama mai sanyaya miki rai, mai goyon tsufanki, gama surukarki wadda take ƙaunarki, wadda ta fiye miki ‘ya’ya maza bakwai, ita ta haife shi.”

16 Sa’an nan Na’omi ta ɗauki yaron ta rungume shi a ƙirjinta, ta zama mai renonsa.

17 Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na’omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda.

Asalin Zuriyar Dawuda

18-22 Wannan shi ne asalin zuriyar Dawuda. Aka fara daga Feresa zuwa Dawuda. Feresa ne mahaifin Hesruna, Hesruna kuma ya haifi Arama, Arama ya haifi Amminadab, Amminadab kuma ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon kuma ya haifi Bo’aza, Bo’aza ya haifi Obida, Obida kuma ya haifi Yesse, sa’an nan Yesse ya haifi Dawuda.