1 SAM 24

Dawuda Ya Bar Saul da Rai a En-gedi

1 Da Saul ya komo daga yaƙi da Filistiyawa, sai aka faɗa masa Dawuda yana jejin En-gedi.

2 Sai Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga cikin dukan mutanen Isra’ila, ya tafi ya nemi Dawuda da mutanensa a gaban duwatsun awakin jeji.

3 Saul ya isa garken tumaki a gefen hanya, inda akwai kogo. Sai ya shiga cikin kogon don ya huta. Dawuda da mutanensa kuwa suna zaune a ƙurewar kogon.

4 Mutanen Dawuda suka ce masa, “Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka yi yadda ka ga dama da shi.” Dawuda kuwa ya tashi a hankali, ya yanke shafin rigar Saul.

5 Daga baya zuciyar Dawuda ta kāshe shi domin ya yanke shafin rigar Saul.

6 Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji ya sawwaƙa in yi wa ubangijina irin abu haka, har in miƙa hannuna in kashe keɓaɓɓe na Ubangiji.”

7 Da wannan magana Dawuda ya rinjayi mutanensa, bai yarda musu su fāɗa wa Saul ba.

Sai Saul ya fita daga kogon ya kama hanya, ya yi tafiyarsa.

8 Daga baya kuma Dawuda ya fita daga kogon, ya yi kira, ya ce, “Ya ubangijina, sarki.” Da Saul ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna.

9 Ya ce wa Saul, “Me ya sa kake kasa kunne ga maganganun mutanen da suke cewa, ‘Dawuda yana nema ya cuce ka?’

10 To, yau da idanunka ka ga yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a kogon, har waɗansu suka ce mini in kashe ka, amma na ji tausayinka. Na ce, ‘Ba zan miƙa hannuna in kashe ubangijina ba, gama shi keɓaɓɓe na Ubangiji ne.’

11 Baba, duba, ga shafin rigarka a hannuna. Tun da yake na yanki shafin rigarka ban kuwa kashe ka ba, sai ka sani ba ni da niyyar yi maka mugunta. Ban yi maka laifi ba, ko da yake kana farautar raina.

12 Ubangiji dai zai shara’anta tsakanina da kai, ya sāke mini, amma hannuna ba zai taɓa ka ba.

13 Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.

14 Shin, sawun wa Sarkin Isra’ila yake bi? Wane ne kuma kake runtuma? Kana bin sawun mataccen kare, da sawun tunkuyau?

15 Ubangiji ne zai zama alƙali, ya hukunta tsakanina da kai. Zai tsaya mini, ya cece ni daga hannunka.”

16 Da Dawuda ya gama faɗa wa Saul wannan magana, sai Saul ya ce, “Ɗana, Dawuda, muryarka ke nan?” Ya yi kuka da ƙarfi.

17 Sa’an nan ya ce wa Dawuda, “Ka fi ni adalci, gama ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.

18 Yau ka nuna a sarari yadda ka yi mini alheri. Ubangiji ya bashe ni a hannunka, amma ba ka kashe ni ba.

19 Idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Ubangiji ya sāka maka saboda alherin da ka yi mini yau.

20 Yanzu kuwa na sani za ka zama sarki, sarautar Isra’ila za ta kahu a hannunka.

21 Sai ka rantse mini da Ubangiji, cewa ba za ka hallaka zuriyata a bayana ba, ba kuwa za ka shafe sunana daga cikin gidan ubana ba.”

22 Dawuda kuwa ya yi wa Saul alkawari.

Sa’an nan Saul ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka koma wurin ɓuya.