Rasuwar Sama’ila
1 Sama’ila kuwa ya rasu. Dukan Isra’ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama.
Dawuda da Abigail
Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran.
2 Akwai wani mutumin Mawon wanda yake da harka a Karmel. Mutumin mai dukiya ne ƙwarai, yana da tumaki dubu uku (3,000) da awaki dubu (1,000). Yana yi wa tumakinsa sausaya a Karmel.
3 Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.
4 Daga cikin jeji, Dawuda ya ji, wai Nabal yana yi wa tumakinsa sausaya,
5 sai ya aiki samari goma, ya ce musu, “Ku tafi Karmel wurin Nabal, ku ce ina gaishe shi.
6 Gaisuwar da za ku yi masa ke nan, ku ce, ‘Salama gare ka, salama ga gidanka, salama kuma ga dukan abin da kake da shi.
7 Na ji kana da masu sausaya. Lokacin da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, ba abin da ya ɓace musu dukan lokacin da suke a Karmel.
8 Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ”
9 Sa’ad da samarin Dawuda suka zo, suka faɗa wa Nabal dukan abin da Dawuda ya ce musu, sai suka dakata.
10 Nabal ya amsa wa barorin Dawuda, ya ce, “Wane ne Dawuda? Wane ne ɗan Yesse? A kwanakin nan akwai barori da yawa waɗanda suka tayar wa iyayengijinsu.
11 Zan ɗauki abincina, da ruwana, da namana wanda na yanka wa masu yi mini sausaya in ba mutanen da ban san inda suka fito ba?”
12 Barorin Dawuda suka koma suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce.
13 Sai Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa ya rataya takobinsa.” Ko wannensu kuwa ya rataya takobi. Dawuda kuma ya rataya nasa takobi. Mutum wajen arbaminya suka tafi tare da shi. Mutum metan kuwa suka zauna a wurin kayayyakinsu.
14 Sai ɗaya daga cikin samarin Nabal ya faɗa wa Abigail, wato matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko manzanninsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.
15 Ga shi, mutanen kuwa sun yi mana kirki, ba mu sha wata wahala ba, ba abin da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su a jeji.
16 Sun zama mana ganuwa dare da rana dukan lokacin da muke tare da su a wurin kiwon tumaki.
17 Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”
18 Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan ‘ya’yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.
19 Ta ce wa samarin, “Ku yi gaba, ga ni nan tafe bayanku.” Amma ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.
20 Tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa tafe. Ta tafi, ta sadu da su.
21 Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abin da yake nasa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.
22 Allah ya buge ni in mutu, idan na bar masa wani mutum da rai kafin gobe da safe.”
23 Da Abigail ta ga Dawuda, sai ta yi sauri ta sauka daga kan jakin, ta durƙusa gabansa har ƙasa.
24 Ta faɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ya shugabana, bari laifin ya zama nawa. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka kuma yarda ka ji maganar baiwarka.
25 Kada maigidana ya kula da Nabal, gama wawa ne, kamar yadda sunansa yake, wato wawa. Ni dai ban ga samarin da ubangijina ya aika ba.
26 Yanzu, ya maigida, na rantse da ran Ubangiji da kuma ranka, ka ga Ubangiji ya hana ka zubar da jini, da ɗaukar wa kanka fansa, sai ka bar maƙiyanka da waɗanda suke nema su cuce ka su zama kamar Nabal.
27 Idan ka yarda ka karɓi kyautan nan da baiwarka ta kawo maka domin a ba samarin da suke tare da kai.
28 Ina roƙonka ka gafarta mini laifina. Ubangiji zai sa ka zama sarki, kai da zuriyarka, kana yin yaƙi na Ubangiji. Ba kuwa za ka aikata wani mugun abu ba a dukan kwanakinka.
29 Idan wani ya tashi tsaye don ya bi sawunka, ya kuma nemi ranka, Ubangiji zai kiyaye ranka, amma rayukan maƙiyanka za a wurga su kamar dutsen majajjawa.
30 Sa’ad da Ubangiji ya cika maka dukan alherin da ya yi maka alkawari, ya kuma naɗa ka Sarkin Isra’ila,
31 ba kuwa za ka sami dalilin baƙin ciki ba, ko damuwar lamiri domin ba ka da alhakin jini, ba ka kuma ɗaukar wa kanka fansa. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, sai ka tuna da ni, baiwarka.”
32 Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abigail, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aike ki ki tarye ni.
33 Basirarki mai albarka ce, ke kuma mai albarka ce, gama kin hana ni zubar da jini da ɗaukar wa kaina fansa yau.
34 Hakika, Ubangiji Allah na Isra’ila ya hana in yi miki ɓarna. Da ba domin kin yi hanzari, kin zo, kin tarye ni ba, da ba wani mutumin Nabal da zai ragu kafin gobe da safe.”
35 Sai Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa. Ya ce mata, “Ki koma gida kada ki damu. Zan yi abin da kike bukata.”
36 Abigail ta koma wurin Nabal, ta iske shi yana biki irin na sarakuna a gidansa. Ya yi ta nishaɗi, ya bugu sosai, don haka ba ta ce masa kome ba sai da safe.
37 Da safe, sa’ad da ruwan inabi ya sake shi, sai Abigail ta faɗa masa abin da ya faru. Zuciyarsa kuwa ta tsinke gaba ɗaya.
38 Bayan kwana goma sai Ubangiji ya bugi Nabal, ya mutu.
39 Sa’ad da Dawuda ya ji Nabal ya mutu, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya sāka mini a kan irin rainin da Nabal ya yi mini. Ya kuma hana ni aikata mugunta. Ya ɗora wa Nabal muguntarsa a kansa.”
Sa’an nan Dawuda ya aika, ya nemi Abigail ta zama matarsa.
40 Da barorin Dawuda suka zo wurin Abigail a Karmel, suka ce mata, “Dawuda ne ya aiko mu wurinki domin mu kai ki wurinsa, ki zama matarsa.”
41 Sai ta rusuna har ƙasa, ta ce, “Ni baranyarsa ce, ina a shirye in wanke ƙafafun barorinsa.”
42 Sai ta yi hanzari ta hau jaki, ta ɗauki kuyanginta, su biyar, ta tafi tare da manzannin Dawuda, ta zama matarsa.
43 Dawuda kuma ya auro Ahinowam Bayezreyeliya, dukansu biyu kuwa suka zama matansa.
44 Amma Saul ya aurar da Mikal, ‘yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake a Gallim.