Dawuda Ya Ci Amalekawa
1 Sa’ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.
2 Suka kwashe mata da dukan waɗanda suke ciki manya da ƙanana, suka tafi da su. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.
3 Da Dawuda da mutanensa suka ga an ƙone garin, an kuma kwashe matansu, da ‘ya’yansu mata da maza ganima,
4 sai suka yi ta kuka da ƙarfi, har ƙarfinsu ya ƙare.
5 An kwashe matan Dawuda biyu ganima, wato Ahinowam Bayezreyeliya da Abigail Bakarmeliya, matar Nabal wanda ya mutu.
6 Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda ‘ya’yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.
7 Sai ya ce wa Abiyata firist, ɗan Ahimelek, ya kawo masa falmaran. Abiyata kuwa ya kawo masa.
8 Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun ‘yan harin nan? Zan ci musu?”
Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”
9-10 Sai Dawuda da mutanensa ɗari shida suka tashi, suka kama hanya, suka kai rafin Besor inda suka bar mutum metan waɗanda suka kāsa. Amma Dawuda da mutum ɗari huɗu suka ci gaba da bin mutanen.
11 Mutanen Dawuda suka sami wani Bamasare a karkara, suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci da ruwa, ya ci ya sha.
12 Suka kuma ba shi kauɗar ɓaure da nonnan inabi biyu. Da ya ci sai ya wartsake, gama ya yi yini uku da dare uku ba ci ba sha.
13 Dawuda kuwa ya tambaye shi, “Wane ne ubangidanka? Daga ina ka fito?”
Ya amsa, ya ce, “Ni saurayi ne, Bamasare, baran wani Ba’amaleke. Kwana uku ke nan da ubangidana ya tafi ya bar ni a baya saboda ba ni da lafiya.
14 Mun kai hari a Negeb ta Keretiyawa ta Yahuza, da Negeb ta Kalibu, muka kuma ƙone Ziklag.”
15 Dawuda ya ce masa, “Za ka yarda ka kai ni wurin maharan nan?”
Sai ya ce wa Dawuda, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan nan suke.”
16 Ya kai Dawuda a wurinsu, sai ga su nan a baje ko’ina a ƙasar, suna ci, suna sha, suna rawa, saboda ganima mai yawa da suka kwashe daga ƙasar Filistiyawa da ƙasar Yahuza.
17 Sai Dawuda ya yi ta karkashe su tun faɗuwar rana har zuwa kashegari da yamma. Ba wanda ya tsira daga cikinsu sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.
18 Dawuda ya ƙwato dukan abin da Amalekawa suka kwashe, har da matansa biyu.
19 Ba abin da ya ɓace, ƙanƙane ko babba, ko cikin ‘ya’ya mata da maza, ko kuwa wani abu daga cikin ganimar, duk Dawuda ya komar da su.
20 Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.”
21 Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bar su a rafin Besor, sai suka tafi su taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su ya gaishe su.
22 Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum ya ɗauki matarsa da ‘ya’yansa ya tafi.”
23 Amma Dawuda ya ce, “’Yan’uwana, ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ubangiji ya kiyaye mu, ya kuma ba da maharan da suka washe mu a hannunmu.
24 Wa zai goyi bayanku a kan wannan al’amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya rabonsu zai zama daidai da juna.”
25 Tun daga wannan rana zuwa gaba, wannan ya zama doka da ka’ida ga Isra’ila.
26 Sa’ad da Dawuda ya komo Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuza, da rabo daga cikin ganimar, ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”
27 Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir,
28 da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa,
29 da Rakal, da garuruwa na Yerameyeliyawa, da garuruwa na Ƙan’aniyawa,
30 da Horma, da Ashan, da Atak,
31 da Hebron, da dukan wuraren da Dawuda da mutanensa suka taɓa tafiya.