1 SAM 31

Rasuwar Saul da ‘Ya’yansa Maza

1 Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa. Isra’ilawa kuma suka yi gudun Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.

2 Filistiyawa suka ci Saul da ‘ya’yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, ‘ya’yan Saul.

3 Yaƙin ya matsa wa Saul. Maharba suka harbe shi, suka yi masa mummunan rauni.

4 Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa.

5 Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya rasu, shi ma ya fāɗa a kan nasa takobi ya mutu tare da Saul.

6 Haka Saul, da ‘ya’yansa maza guda uku, da mai ɗaukar masa makamai, da dukan mutanen da suke tare da shi suka mutu a rana ɗaya.

7 Sa’ad da Isra’ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra’ila sun gudu, Saul kuma da ‘ya’yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.

8 Da Filistiyawa suka zo kashegari don su washe kayan kisassun, sai suka tarar da gawar Saul da gawawwakin ‘ya’yansa uku a kan Dutsen Gilbowa.

9 Suka yanke kansa, suka tuɓe makamansa. Suka aika manzannin a ƙasar Filistiyawa da suke kusa don su kai wannan albishir zuwa ga haikalin gumakansu, da mutanensu.

10 Suka ajiye makaman Saul cikin haikalin gumakan nan Ashtarot. Suka ɗaure gawarsa a kan garun Bet-sheyan.

11 Da mazaunan Yabesh-gileyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,

12 sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin ‘ya’yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can.

13 Suka binne ƙasusuwansu a gindin itacen tsamiya a Yabesh, sa’an nan suka yi azumi kwana bakwai.