1 SAR 15

Sarki Abaija na Yahuza

1 A shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yerobowam ɗan Nebat, Abaija ya sarauci mutanen Yahuza.

2 Ya yi mulki shekara uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma’aka, ‘yar Absalom, wato kakarsa.

3 Shi kuma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa sosai, kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi ba.

4 Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima,

5 domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.

6 Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.

7 Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

8 Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.

Sarki Asa na Yahuza

9 A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra’ila, Asa ya sarauci jama’ar Yahuza.

10 Ya yi shekara arba’in da ɗaya yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma’aka, ‘yar Absalom, wato kakarsa.

11 Asa kuwa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.

12 Ya kori mata da maza da suke karuwanci a wuraren tsafi na arna a ƙasar, ya kuma kawar da gumakan da kakanninsa suka yi.

13 Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma’aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.

14 Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba, duk da haka Asa ya yi aminci sosai ga Ubangiji dukan kwanakinsa.

15 Ya kawo dukan tsarkakakkun abubuwan da tsohonsa ya keɓe, da kuma azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi, a cikin Haikalin Ubangiji.

Alkawari Tsakanin Asa da Ben-hadad

16 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha, Sarkin Isra’ila a dukan kwanakin mulkinsu.

17 Ba’asha, Sarkin Isra’ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.

18 Sa’an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce,

19 “Bari mu ƙulla alkawari da juna kamar yadda tsohona da tsohonka suka yi, ga shi, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Sai ka tafi, ka warware alkawarinka da Ba’asha, Sarkin Isra’ila, domin ya tashi ya bar ni.”

20 Ben-hadad kuwa ya yarda da maganar sarki Asa. Ya kuwa aiki shugabannin sojojinsa su yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Su kuwa suka tafi, suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma’aka, da dukan Kinneret, da dukan ƙasar Naftali.

21 Da Ba’asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.

22 Sa’an nan sarki Asa ya gayyaci dukan jama’ar Yahuza, ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi suka kwashe duwatsu da katakai waɗanda Ba’asha yake ginin Rama da su. Da su sarki Asa ya gina Geba ta Biliyaminu, da Mizfa.

23 Sauran dukan ayyukan Asa, da dukan ƙarfinsa, da dukan abin da ya yi, da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. Amma da ya tsufa, sai ya sami ciwo a ƙafafunsa.

24 Asa kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima, Ɗansa Yehoshafat ya gāji sarautarsa.

Sarki Nadab na Isra’ila

25 Nadab ɗan Yerobowam ya ci sarautar Isra’ila a shekara ta biyu ta sarautar Asa Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra’ila shekara biyu.

26 Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra’ila su yi zunubi.

27 Ba’asha ɗan Ahija kuwa daga gidan Issaka ya yi wa Nadab maƙarƙashiya, ya kashe shi a Gibbeton ta Filistiyawa, gama Nadab da mutanen Isra’ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi.

28 Haka Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, ya kuwa ci sarautar a maimakonsa.

29 Nan da nan da ya zama sarki, sai ya kashe dukan mutanen gidan Yerobowam, bai bar wani na gidan Yerobowam da rai ba, ya hallaka su sarai, bisa ga maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa bawansa Ahija mutumin Shilo.

30 Wannan abu ya faru saboda zunubin Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra’ila su yi, ya tsokani fushin Ubangiji Allah na Isra’ila.

31 Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

32 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba’asha Sarkin Isra’ila dukan kwanakin sarautarsu.

Sarki Ba’asha na Isra’ila

33 A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba’asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra’ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta.

34 Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra’ila su yi.