1 SAR 22

Mikaiya Ya Yi wa Ahab Kashedi

1 Aka yi shekara uku ba a yi yaƙi tsakanin Suriya da Isra’ila ba.

2 A shekara ta uku ɗin, sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya ziyarci Sarkin Isra’ila.

3 Sarkin Isra’ila kuwa ya ce wa fādawansa, “Ko kun sani Ramot-gileyad tamu ce, ga shi kuwa, mun yi shiru, ba mu ƙwace ta daga hannun Sarkin Suriya ba?”

4 Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?”

Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra’ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.”

5 Yehoshafat ya ce wa Sarkin Isra’ila, “Ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”

6 Sa’an nan Sarkin Isra’ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?”

Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”

7 Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin da za mu tambaya kuma?”

8 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.”

Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”

9 Sa’an nan Sarkin Isra’ila ya kirawo wani bafāde, ya ce masa, “Maza, ka taho da Mikaiya ɗan Imla.”

10 Sarkin Isra’ila da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune a kujerun sarautarsu, saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya. Annabawa kuwa suna annabci a gabansu.

11 Zadakiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.’ ”

12 Dukan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot, za ka yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”

13 Bafāden da ya tafi kiran Mikaiya ya ce masa, “Ga shi, maganar sauran annabawan iri ɗaya ce, sun yi maganar alheri ga sarki, sai kai ma ka yi magana irin tasu, ka yi maganar alheri ga sarki.”

14 Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”

15 Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?”

Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”

16 Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”

17 Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra’ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”

18 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, ba zai yi wani annabcin alheri a kaina ba sai dai na masifa?”

19 Makaiya kuwa ya ce, “Ka ji maganar Ubangiji, gama na ga Ubangiji yana zaune a kursiyinsa. Dukan taron mala’ikun Sama suna tsaye a wajen damansa da na hagunsa.

20 Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai yaudari Ahab, ya tafi ya fāɗa wa Ramot?’ Sai wannan ya ce abu kaza, wani kuma ya ce abu kaza,

21 har da wani ruhu ya fito ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Ni zan yaudare shi.’

22 Ubangiji ya ce masa, ‘Ta wace hanya?’ Sai ruhun ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ba shakka za ka yaudare shi, za ka yi nasara, sai ka tafi.’ ”

23 Mikaiya ya ce, “Ga abin da ya faru, Ubangiji ya bar annabawanka su faɗa maka ƙarya. Amma Ubangiji kansa ya riga ya zartar maka da masifa.”

24 Sa’an nan Zadakiya ɗan Kena’ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”

25 Mikaiya ya ce masa, “A ran nan za ka gani, ka kuma gudu ka shiga har ƙurewar ɗaki don ka ɓuya.”

26 Sarki Ahab ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki.

27 Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”

28 Mikaiya kuwa ya ce, “In dai ka komo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana da ni ba.” Ya ƙara da cewa, “Kowa ya kasa kunne ga abin da na faɗa.”

Mutuwar Ahab

29 Ahab Sarkin Isra’ila da Sarkin Yahuza suka tafi Ramot-gileyad.

30 Sarkin Isra’ila kuwa ya ce wa Sarkin Yahuza, “Zan ɓad da kama in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafinka na sarauta.” Sai Ahab ya ɓad da kama ya tafi wurin yaƙi.

31 Sarkin Suriya dai ya riga ya umarci shugabannin karusan yaƙinsa, su talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da kowa, kome matsayinsa, sai dai Ahab kaɗai.”

32 Sa’ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, sai suka ce, “Lalle shi ne Ahab.” Sai suka juya don su yi yaƙi da shi. Yehoshafat kuwa ya yi ihu.

33 Da shugabannin karusan yaƙi suke gane ba Ahab ba ne, sai suka rabu da shi.

34 Wani sojan Suriya kuwa ya yi sa’a, ya shilla kibiya kawai, sai ta sami Ahab, ta kafar sulkensa. Saboda haka ya ce wa mai korar karusarsa, “Ka juya, ka fitar da ni daga fagen fama gama an yi mini rauni.”

35 A ran nan yaƙi ya yi tsanani. Aka tallafi Ahab a cikin karusarsa a gaban Suriyawa. Da maraice ya mutu. Jinin raunin da aka yi masa ya zuba a cikin karusar.

36 A wajen faɗuwar rana aka yi wa sojoji shela aka ce, “Kowa ya koma garinsu da ƙasarsu.”

37 Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, aka binne shi.

38 Suka wanke karusarsa a tafkin Samariya. Karnuka suka lashe jininsa, karuwai kuma suka yi wanka a tafkin kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

39 Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

40 Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.

Sarki Yehoshafat na Yahuza

41 Yehoshafat ɗan Asa ya ci sarautar Yahuza a shekara ta huɗu ta sarautar Ahab, Sarkin Isra’ila.

42 Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba ‘yar Shilhi.

43 Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan.

44 Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra’ila amana.

45 Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

46 Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.

47 A lokacin babu sarki a Edom sai wakili.

48 Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber.

49 Sa’an nan Ahaziya, ɗan Ahab, ya ce wa Yehoshafat. “Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage.” Amma Yehoshafat bai yarda ba.

50 Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.

Sarki Ahaziya na Isra’ila

51 Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra’ila shekara biyu.

52 Ya yi zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi halin tsohonsa da na tsohuwarsa, da na Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila su yi zunubi.

53 Ya bauta wa gunkin nan Ba’al ya yi masa sujada. Ya kuma sa Ubangiji Allah na Isra’ila ya yi fushi, gama ya bi halin tsohonsa.