1 TAR 15

An Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima

1 Dawuda kuwa ya gina wa kansa gidaje a birninsa, ya kuma kafa alfarwa domin akwatin alkawari na Allah.

2 Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.”

3 Saboda haka Dawuda ya tattara Isra’ilawa duka a Urushalima don a kawo akwatin alkawarin Ubangiji a wurinsa, inda aka riga aka shirya masa.

4 Dawuda kuma ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya, tare kuma da Lawiyawa.

5 Waɗanda aka tattaro ke nan, daga iyalin Kohat su ɗari da shirin ne. Uriyel shi ne shugabansu.

6 Daga iyalin Merari su ɗari biyu da ashirin, Asaya ne shugabansu.

7 Daga iyalin Gershon ɗari da talatin, Yowel ne shugabansu.

8 Daga iyalin Elizafan ɗari biyu, Shemaiya ne shugabansu.

9 Daga iyalin Hebron su tamanin, Eliyel ne shugabansu.

10 Daga iyalin Uzziyel ɗari da goma sha biyu, Amminadab ne shugabansu.

11 Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyata firistoci, da Lawiyawa, wato Uriyel, da Asaya, da Yowel, da Shemaiya, da Eliyel, da Amminadab,

12 ya ce musu, “Ku ne shugabanni na gidajen kakanninku, Lawiyawa. Sai ku tsarkake kanku da ‘yan’uwanku domin ku iya kawo akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a inda na shirya masa.

13 Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”

14 Sa’an nan firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji Allah na Isra’ila.

15 Lawiyawa fa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah a bisa sandunansa a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.

16 Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa ‘yan’uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske.

17 Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berikiya daga cikin ‘yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kishi.

18 Daga cikin ‘yan’uwansu, har yanzu aka zaɓi mataimakansu, wato Zakariya, da Ben, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Benaiya, da Ma’aseya, da Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da masu tsaron ƙofofi.

19 Haka aka zaɓi mawaƙa, wato Heman, da Asaf, da Etan don su buga kuge na tagulla.

20 Su Zakariya, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Ma’aseya, da Benaiya, su ne masu kaɗa molaye da murya a sama.

21 Su Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da Azaziya suke ja da garayu da murya ƙasa-ƙasa.

22 Kenaniya shugaban Lawiyawa shi ne yake bi da waƙoƙi domin shi gwani ne.

23 Berikiya da Elkana su ne masu tsaron ƙofa ta akwatin alkawari.

24 Sai Shebaniya, da Yehoshafat, da Netanel, da Amasai, da Zakariya, da Benaiya, da Eliyezer, firistoci, suka yi ta busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-edom da Yehiya su ne kuma masu tsaron ƙofar akwatin alkawari.

25 Haka Dawuda, da dattawan Isra’ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom.

26 Saboda Allah ya taimaki Lawiyawa waɗanda suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai.

27 Dawuda yana saye da kyakkyawar taguwa ta lilin tare da Lawiyawa duka waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, da mawaƙa, da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dawuda kuma ya sa falmaran ta lilin.

28 Da haka fa Isra’ilawa duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.

29 Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shigo birnin Dawuda, sai Mikal ‘yar Saul ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana ta rawa, yana murna, sai ta ji ya saƙale mata a zuci.