1 TAR 19

Dawuda ya Ci Ammonawa da Suriyawa

1 Bayan haka kuma Nahash Sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa kuma ya gāji sarautarsa.

2 Sa’an nan Dawuda ya ce, “Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahash, gama tsohonsa ya nuna mini alheri.” Don haka Dawuda ya aiki manzanni su yi wa Hanun ta’aziyyar rasuwar tsohonsa.

Fādawan Dawuda suka zo ƙasar Ammon wurin Hanun, domin su yi masa ta’aziyya.

3 Amma hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne da ya aiko manzanni su yi maka ta’aziyya? Fādawansa sun zo wurinka ne don su leƙi asirin ƙasar, su bincike ta, su ci ta da yaƙi.”

4 Hanun kuwa ya kama fādawan Dawuda, ya aske gyammansu, ya yanyanke rigunansu a tsaka daga wajen kwankwaso, sa’an nan ya sallame su.

5 Waɗansu mutane kuwa suka je suka faɗa wa Dawuda abin da ya sami mutanen. Sai ya aiko a tarye su, gama an ƙasƙanta mutanen nan da gaske. Sai sarki ya ce, “Ku zauna a Yariko, har lokacin da gyammanku suka tohu sa’an nan ku iso.”

6 Sa’ad da Ammonawa suka ga sun mai da kansu abin ƙi ga Dawuda, sai Hanun da Ammonawa suka aika da talanti dubu (1,000) na azurfa don su yi ijara da karusai da mahayan dawakai daga Mesofotamiya, da jihohin Ma’aka ta Suriya, da Zoba.

7 Suka yi ijarar karusai dubu talatin da dubu biyu (32,000), da Sarkin Ma’aka, tare da jama’arsa. Suka zo suka kafa sansani a gaban Medeba. Ammonawa kuwa suka tattaru daga biranensu don su yi yaƙi.

8 Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab tare da dukan sojoji, ƙarfafan mutane.

9 Sai Ammonawa suka fito suka jā dāga a ƙofar birninsu. Sarakunan da suka zo suka ware suka zauna a saura.

10 Da Yowab ya ga an kafa masa yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu jarumawa na gaske a Isra’ila, ya sa su su kara da Suriyawa.

11 Sa’an nan ya sa sauran sojoji a hannun Abishai ɗan’uwansa. Suka jā dāgar yaƙi da Ammonawa.

12 Yowab ya ce wa Abishai, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, to, sai ka taimake ni, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinka, to, sai in taimake ka.

13 Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama’armu da biranen Allahnmu. Bari Ubangiji ya yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”

14 Yowab da jama’ar da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Suriyawa, sai Suriyawa suka gudu daga gabansu.

15 Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai, ɗan’uwan Yowab, suka shiga birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima.

16 Da Suriyawa suka ga Isra’ilawa sun ci su da yaƙi sai suka aiki manzanni suka kira Suriyawa waɗanda suke hayin kogi. Shobak shugaban sojojin Hadadezer ne yake shugabantarsu.

17 Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda, sai ya tattara Isra’ilawa duka ya haye Urdun, ya zo wurinsu, ya jā dāga don ya yi yaƙi da su. Aka fara gabza yaƙi,

18 sai Suriyawa suka gudu a gaban Isra’ilawa, Dawuda ya karkashe Suriyawa, mutum dubu bakwai (7,000) masu karusai, da sojojin ƙasa dubu arba’in (40,000). Ya kuma kashe Shobak shugaban sojojin.

19 Da barorin Hadadezer suka ga Isra’ilawa sun ci su da yaƙi, sai suka ƙulla zumunci da Dawuda, suka bauta masa. Saboda haka Suriyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba.