Dawuda ya ci Ammonawa da Suriyawa
1 Sa’ad da Sarkin Ammonawa, wato Nahash, ya rasu, sai Hanun ɗansa ya gāje shi.
2 Dawuda ya ce, “Zan yi wa Hanun alheri kamar yadda tsohonsa ya yi mini.” Dawuda kuwa ya aiki manzanni su yi masa ta’aziyya.
Amma da suka isa can,
3 sai hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne, da ya aiko manzanninsa su yi maka ta’aziyya? Ai, manzannin nan da ya aiko ‘yan leƙen asirin ƙasa ne. Sun zo ne su bincika don su san yadda za a ci birnin.”
4 Sai Hanun ya sa aka aske wa manzannin nan na Dawuda rabin gyammansu suka kuma yanyanke rigunansu daidai ɗuwawu, sa’an nan suka sallame su.
5 Da aka faɗa wa Dawuda sai ya aika a tarye su, gama mutanen sun sha kunya ƙwarai. Sarki Dawuda ya ce musu su zauna a Yariko har gyammansu su toho, sa’an nan su komo.
6 Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma’aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000).
7 Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab da dukan rundunar jarumawan.
8 Ammonawa suka fita suka ja dāgar yaƙi a ƙofar garin, amma Suriyawan Zoba da na Rehob, da mutanen Ish-tobi da na Ma’aka suka ja tasu dāgar a karkara.
9 Da Yowab ya ga an ja masa dāgar yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu Isra’ilawa, ya sa su gabza da Suriyawa.
10 Sauran mutane kuwa ya sa su a hannun Abishai, ƙanensa. Ya sa su gabza da Ammonawa.
11 Ya ce musu, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, ku kawo mini gudunmawa, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinku, sai in kai muku gudunmawa.
12 Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama’armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”
13 Sa’an nan Yowab da mutanensa suka matsa, su gabza da Suriyawa. Suriyawa kuwa suka gudu.
14 Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.
15 Sa’ad da Suriyawa suka ga Isra’ilawa sun ci su, suka tattara kansu.
16 Hadadezer ya aika aka kawo Suriyawan da suke a hayin Kogin Yufiretis. Suka taru a Helam. Shobak shugaban rundunar Hadadezer shi ne ya shugabance su.
17 Sa’ad da Dawuda ya ji labari, ya tara Isra’ilawa duka, ya haye Urdun zuwa Helam. Suriyawa kuwa suka ja dāgar yaƙi, suka yi yaƙi da Dawuda.
18 Amma Suriyawa suka gudu daga gaban Isra’ilawa. Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa, mahayan karusai ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba’in (40,000). Aka yi wa Shobak shugaban rundunarsu rauni wanda ya zama ajalinsa, a can ya rasu.
19 Sa’ad da dukan hakiman Hadadezer suka ga Isra’ilawa sun ci su, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa. Suka zama talakawansu. Wannan ya sa Suriyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudunmawa.