Dawuda ya Nuna wa Mefiboshet Alheri
1 Dawuda ya yi tambaya, ko akwai wani da ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna wa alheri saboda Jonatan.
2 Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?”
Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”
3 Sa’an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah.
Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”
4 Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?”
Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.”
5 Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.
6 Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!”
Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”
7 Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”
8 Mefiboshet kuwa ya rusuna, ya ce, “Ni wane ne har da za ka kula da ni, ni da ban fi mataccen kare daraja ba?”
9 Sa’an nan sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, “Dukan abin da yake na Saul, da dukan abin da yake na iyalinsa, na ba ɗan maigidanka.
10 Kai, da ‘ya’yanka maza, da barorinka za ku riƙa yi wa iyalin Saul noma, ku kawo musu amfanin domin su sami abinci, amma Mefiboshet kansa, zai riƙa cin abinci a teburina kullum.” (Ziba kuwa yana da ‘ya’ya maza goma sha biyar, da barori ashirin.)
11 Ziba ya amsa wa sarki, ya ce, “Baranka zai yi dukan abin da sarki ya umarta.”
Mefiboshet kuwa ya riƙa cin abinci a teburin sarki kamar ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarkin.
12 Mefiboshet yana da ɗa sunansa Mika. Dukan waɗanda suke zaune a gidan Ziba kuma suka zama barorin Mefiboshet.
13 Mefiboshet kuwa ya zauna a Urushalima ya riƙa cin abinci a teburin sarki kullum. Dukan ƙafafunsa kuwa sun naƙasa.