2 SAR 15

Sarki Azariya na Yahuza

1 A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam na biyu Sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

2 Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara hamsin da biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa, Yekoliya ta Urushalima.

3 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda Amaziya, tsohonsa, ya yi.

4 Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai.

5 Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama’ar ƙasar.

6 Sauran ayyukan Azariya, da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

7 Azariya ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Yotam ɗansa ya gāji sarautarsa.

Sarki Zakariya na Isra’ila

8 A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Zakariya ɗan Yerobowam na biyu, ya ci sarautar Isra’ila a Samariya wata shida.

9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

10 Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa’an nan ya hau gadon sarautarsa.

11 Sauran ayyukan da Zakariya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

12 Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa ‘ya’yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra’ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.

Sarki Shallum na Isra’ila

13 Shallum ɗan Yabesh ya ci sarauta a shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza. Ya yi mulki wata ɗaya a Samariya.

14 Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa.

15 Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

16 A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.

Sarki Menahem na Isra’ila

17 A shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya, Sarkin Yahuza, Menahem ɗan Gadi, ya ci sarautar. Ya yi shekara goma a Samariya.

18 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A dukan kwanakinsa bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

19 Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai.

20 Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra’ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.

21 Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

22 Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.

Sarki Fekahiya na Isra’ila

23 A shekara ta hamsin ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Fekahiya ɗan Menahem, ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara biyu.

24 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

25 Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.

26 Sauran ayyukan Fekahiya, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

Sarki Feka na Isra’ila

27 A shekara ta hamsin da biyu ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Feka ɗan Remaliya ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara ashirin.

28 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

29 A zamanin Feka Sarkin Isra’ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma’aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa’an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.

30 Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa’an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya.

31 Sauran ayyukan Feka da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

Sarki Yotam na Yahuza

32 A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

33 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha, ‘yar Zadok.

34 Yotam ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Azariya, ya yi.

35 Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.

36 Sauran ayyukan Yotam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

37 A kwanakin nan Ubangiji ya fara aiken Rezin Sarkin Suriya da Feka ɗan Remaliya su yi yaƙi da Yahuza.

38 Yotam ya rasu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.