2 SAR 18

Sarki Hezekiya na Yahuza

1 A shekara ta uku ta sarautar Hosheya ɗan Ila Sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz Sarkin Yahuza ya ci sarautar.

2 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abi, ‘yar Zakariya.

3 Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.

4 Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama’ar Isra’ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.

5 Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa.

6 Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa.

7 Ubangiji kuwa ya kasance tare da shi, duk inda ya nufa sai ya sami albarka. Ya tayar wa Sarkin Assuriya, ya ƙi bautar masa.

8 Ya kuma bugi Filistiyawa har zuwa Gaza da iyakarta daga hasumiya zuwa birni mai garu.

Faɗuwar Samariya

9 A shekara ta huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, a lokacin Hosheya ɗan Ila, Sarkin Isra’ila, yana da shekara bakwai da sarauta, sai Shalmanesar Sarkin Assuriya ya kawo wa Samariya yaƙi, ya kewaye ta.

10 A ƙarshen shekara ta uku, ya ci ta da yaƙi. A lokacin Hezekiya yana da shekara shida da sarauta, Hosheya kuwa yana da shekara tara da tasa sarauta.

11 Sarkin Assuriya kuwa ya kwashi Isra’ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.

12 Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.

Assuriyawa Sun Yi wa Urushalima Barazana

13 A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su.

14 Sai Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya aika zuwa wurin Sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka ƙyale ni, duk abin da ka ɗora mini zan ɗauka.” Sai Sarkin Assuriya ya ce wa Hezekiya Sarkin Yahuza ya ba shi talanti ɗari uku na azurfa, da talanti talatin na zinariya.

15 Hezekiya kuwa ya ba shi dukan azurfar da take cikin Haikalin Ubangiji, da wanda yake cikin baitulmali na gidan sarki.

16 A lokacin sai Hezekiya ya kankare zinariyar da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin Haikalin Ubangiji da ita, ya ba Sarkin Assuriya.

17 Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki.

18 Sa’ad da suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka fito.

19 Sa’an nan Rabshake ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya, cewa mai girma, Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ga wa kake dogara?

20 Kana tsammani maganganu kurum su ne dabara da ƙarfin yin yaƙi? To, ga wa ka dogara har da ka tayar mini?

21 Ga shi yanzu, kana dogara ga Masar, wannan karyayyen sandan kyauro, wanda yakan yi wa hannun mutumin da yake tokarawa da shi sartse. Haka Fir’auna Sarkin Masar, yake ga dukan waɗanda suke dogara gare shi.’

22 “Amma idan ka ce mini, ‘Ina dogara ga Ubangiji Allahnmu,’ to, ba masujadansa na kan tuddai da bagadansa ne Hezekiya ya rurrushe ba? Yana ce wa mutanen Yahuza da Urushalima, ‘Za ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima?’

23 Sai ka zo, ku daidaita da ubangidana, Sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu (2,000), idan za ka iya samun mahayansu.

24 Ba ka isa ka kara da ko mafi ƙanƙanta na shugabannin sojojin maigidana ba, amma har kana dogara ga Masar don samun karusai da mahaya?

25 Kana tsammani, ba da yardar Ubangiji ba ne na kawo wa wurin nan yaƙi don a hallaka shi? Gama Ubangiji ya ce mini, ‘Ka kai wa wannan ƙasa yaƙi don ka hallaka ta.’ ”

26 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa, suka ce wa Rabshake, “Muna roƙonka, ka yi magana da mu barorinka da harshen Aramiya gama muna jinsa, kada ka yi magana da mu da harshen Yahudanci, har mutanen da suke kan garu su ji.”

27 Amma Rabshake ya ce musu, “Ai, ubangidana bai aike ni in yi wannan magana ga ubangidanku da ku kaɗai ba, amma ga dukan mutanen da suke zaune a kan garu, waɗanda aka ƙaddara su tare da ku don su ci najasarsu su sha fitsarinsu.”

28 Sa’an nan Rabshake ya tsaya, ya yi kira da ƙarfi da harshen Yahudanci, ya ce, “Ku ji maganar mai girma, Sarkin Assuriya!

29 Sarki ya ce, ‘Kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, gama ba zai iya cetonku daga hannuna ba.

30 Kada kuma ku yarda Hezekiya ya sa ku dogara ga Ubangiji da cewa lalle Ubangiji zai cece ku, ba za a kuma ba da wannan birni a hannun Assuriya ba.’

31 Kada ku kasa kunne ga Hezekiya, gama Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ku yi amana da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ‘ya’yan inabinsa da ‘ya’yan ɓaurensa, ya kuma sha ruwa daga cikin randarsa,

32 har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi,da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku.

33 Ko akwai wani allah daga cikin allolin al’ummai, wanda ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun Sarkin Assuriya?

34 Ina allolin Hamat, da na Arfad, da na Sefarwayim, da na Hena, da na Iwwa? Sun ceci Samariya daga hannuna ne?

35 Daga cikin dukan allolin ƙasashe, wane ne ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannuna har da Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?’ ”

36 Sai mutanen suka yi tsit, ba wanda ya ce masa uffan, gama sarki ya umarta cewa kada a tanka masa.

37 Sa’an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.