2 TAR 18

Annabi Mikaiya Ya Gargaɗi Ahab

1 Yehoshafat ya arzuta, ya kuma sami ɗaukaka sai ya yi ma’amala da Ahab ta wurin aurayya.

2 Bayan ‘yan shekaru sai ya kai wa Ahab ziyara a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki masu yawan gaske, da bijimai da yawa, domin Yehoshafat da mutanen da suke tare da shi. Ahab ya rinjaye shi don su fāɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi.

3 Sai Ahab, Sarkin Isra’ila, ya ce wa Yehoshafat, Sarkin Yahuza, “Za ka tafi tare da ni zuwa Ramot-gileyad?”

Sai ya amsa, ya ce, “Ni ma kamarka ne, jama’ata kuma kamar jama’arka ce, za mu je yaƙin tare da kai.”

4 Yehoshafat kuma ya ce wa Sarkin Isra’ila, “Sai ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”

5 Ahab kuwa ya tattara annabawa, mutum ɗari huɗu, ya ce musu, “Mu je mu faɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi, ko in haƙura?”

Sai suka ce, “Ka tafi, gama Allah zai ba da ita a hannun sarki.”

6 Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji a nan wanda za mu tambaye shi kuma?”

7 Sai Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Akwai sauran mutum guda wanda za mu iya neman nufin Ubangiji daga gare shi, shi ne Mikaiya, ɗan Imla, amma na ƙi shi saboda ba ya yin annabcin kirki a kaina, sai dai na rashin alheri kullum.”

Amma Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”

8 Sa’an nan Sarkin Isra’ila ya kira wani jarumi ya ce masa, “Maza ka kawo Mikaiya ɗan Imla.”

9 A sa’an nan Sarkin Isra’ila, da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune kowa a gadon sarautarsa, kowane ya caɓa ado, suna kuwa zaune a filin da yake ƙofar Samariya. Dukan annabawa kuwa suna ta yin annabci a gabansu.

10 Sai Zadakiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Suriyawa har su hallaka!’ ”

11 Dukan annabawa kuma suka yi annabci, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot-gileyad ka ci nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannun sarki.”

12 Jarumin fa da ya je ya kira Mikaiya ɗin, ya ce masa, “Ka kula fa, dukan maganganun da annabawa suke yi, sun yi wa sarki daɗi. Don haka kai ma ka yi maganar da za ta gamshi sarki kamar yadda suka yi.”

13 Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji abin da Allahna ya faɗa mini, shi zan faɗa.”

14 Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?”

Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”

15 Amma sarki ya ce masa, “Har sau nawa zan rantsar da kai don kada ka faɗa mini kome, sai gaskiya da sunan Ubangiji?”

16 Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra’ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, ‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.’ ”

17 Sarkin Isra’ila fa ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, cewa ba zai yi annabcin alheri game da ni ba, sai na rashin alheri?”

18 Sai Mikaiya ya ce, “Ji maganar Ubangiji, na ga Ubangiji yana zaune a bisa kursiyinsa, dukan rundunan sama suna tsaye dama da shi da hagu da shi.

19 Sai Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab, Sarkin Isra’ila, don ya haura zuwa Ramot-gileyad ya fāɗi?’ Sai wannan ya faɗi abu kaza, wancan kuma ya faɗi abu kaza.

20 Sai wani ruhu ya zo ya tsaya a gaban Ubangiji, ya ce, ‘Ni zan ruɗe shi.’ Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Ta ƙaƙa?’

21 Sai ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sa’an nan Ubangiji ya ce, ‘To, za ka ruɗe shi har ka yi nasara. Je ka, ka yi haka nan.’

22 “Saboda haka Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan annabawanka, gama Ubangiji ya faɗa, masifa za ta same ka.”

23 Sai Zadakiya ɗan Kena’ana, ya matso ya mari Mikaiya a kumatu ya ce, “Ta wace hanya ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai.”

24 Mikaiya kuwa ya ce, “Za ka gani a ranar da ka shiga ƙuryar ɗaki na can ciki don ɓuya.”

25 Sai Sarkin Isra’ila ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku komar da shi wurin Amon mai mulkin birnin, da yarima Yowash.

26 Ku ce, ‘Sarki ya ce ku sa wannan mutum a kurkuku, ku ciyar da shi da ɗan abinci da ruwa kaɗan har in komo lafiya.’ ”

27 Sai Mikaiya ya ce, “Idan har ka komo lafiya, wato Ubangiji bai yi magana da ni ba ke nan.” Sai ya ce, “Ku ji, ya ku jama’a duka.”

Mutuwar Ahab

28 Sarkin Isra’ila fa, da Yehoshafat Sarkin Yahuza, suka haura zuwa Ramot-gileyad.

29 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama, in shiga yaƙi, amma kai, sai ka sa rigunanka.” Sarkin Isra’ila kuwa ya ɓad da kama, suka shiga yaƙi.

30 Sarkin Suriya ya umarci shugabannin karusansa, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da yaro ko babba, sai dai da Sarkin Isra’ila, shi kaɗai.”

31 Sa’ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, suka ce, “Wannan ne Sarkin Isra’ila,” sai suka juya suka yi yaƙi da shi. Amma Yehoshafat ya yi kururuwa, Ubangiji Allah ya kuɓutar da shi, Allah kuwa ya kawar da su daga gare shi.

32 Da shugabannin karusai suka ga, ashe, ba Sarkin Isra’ila ba ne, sai suka daina binsa suka juyo.

33 Amma wani mutum ya harba kibiya haka kawai, ya sami Sarkin Isra’ila a mahaɗin kafaɗa. Sai sarkin ya ce wa wanda yake korar karusarsa, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin, gama an yi mini rauni.”

34 Ran nan yaƙin ya tsananta, Sarkin Isra’ila kuma ya jingina a cikin karusarsa, yana fuskantar Suriyawa har maraice, rana na fāɗuwa yana rasuwa.