2 TAR 33

Sarki Manassa na Yahuza

1 Manassa yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana mulki a Urushalima.

2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya yi irin ayyukan banƙyama da al’ummai waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban jama’ar Isra’ila suke yi.

3 Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba’al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu.

4 Ya kuma giggina bagadai a cikin Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima sunana zai kasance har abada.”

5 Ya giggina bagadai ga dukan rundunar sama a farfajiyan nan biyu na cikin Haikalin Ubangiji.

6 Ya miƙa ‘ya’yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha’ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.

7 Sai ya kafa gunkin da ya yi a cikin Haikalin Allah, wanda Allah ya faɗa wa Dawuda da ɗansa Sulemanu ya ce, “A cikin wannan Haikali da a Urushalima, inda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila, zan sa sunana har abada.

8 Ba zan ƙara fitar da Isra’ila daga ƙasar da na ba kakanninku ba, in dai sun lura, sun kiyaye, sun aikata dukan abin da na umarce su, da dukan shari’a, da dokoki, da ka’idodi da aka bayar ta hannun Musa.”

9 Ta haka kuwa Manassa ya lalatar da Yahuza da mazaunan Urushalima. Suka aikata muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama’ar Isra’ila.

Tuban Manassa

10 Ubangiji fa ya yi magana da Manassa da jama’arsa, amma ba wanda ya kula.

11 Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.

12 Amma sa’ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.

13 Sa’ad da ya yi addu’a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa’an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.

14 Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa’an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza.

15 Ya kwashe gumaka da siffofi daga cikin Haikalin Ubangiji, da dukan bagadan da ya giggina a bisa dutse na Haikalin Ubangiji da a Urushalima. Ya zubar da su a bayan birnin.

16 Ya kuma komar da bagaden Ubangiji, ya miƙa hadayu na salama da na godiya, ya kuma umarci Yahuza ta bauta wa Ubangiji Allah na Isra’ila.

17 Duk da haka dai jama’a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadai, amma ga Ubangiji Allahnsu kaɗai.

Ƙarshen Mulkin Manassa

18 Sauran ayyukan Manassa, da addu’o’insa zuwa ga Allahnsa, da abubuwan da masugani suka faɗa sa’ad da suka yi masa magana da sunan Ubangiji Allah na Isra’ila, suna cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

19 Addu’arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai.

20 Haka fa Manassa ya rasu, suka binne shi a gidansa, sai Amon ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Sarki Amon na Yahuza

21 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara biyu yana mulki a Urushalima.

22 Shi ma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Manassa, tsohonsa, ya yi. Amon ya miƙa hadaya ga dukan siffofin da tsohonsa, Manassa, ya yi ya bauta musu.

23 Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.

24 Sai fadawansa suka yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.

25 Jama’ar ƙasar kuwa suka karkashe dukan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar, suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gāji gadon sarautarsa.