AYU 19

Bangaskiyar Ayuba Ta Sa Allah Zai Goyi Bayansa

1 Ayuba ya amsa.

2 “Me ya sa kuke azabta ni da maganganu?

3 A kowane lokaci kuna wulakanta ni,

Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.

4 Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne,

Da me ya cuce ku?

5 Tsammani kuke kun fi ni ne,

Kuna ɗauka cewa wahalar da nake sha

Ta tabbatar ni mai laifi ne.

6 Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini,

Ya kafa tarko don ya kama ni.

7 Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba,

Amma ba wanda ya kasa kunne.

Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.

8 Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa,

Ya rufe hanyata da duhu,

9 Gama ya kwashe dukiyata duka,

Ya ɓata mini suna.

10 Ya mammangare ni,

Ya tumɓuke sa zuciyata,

Ya bar ni in yi yaushi, in mutu.

11 Allah ya zaburo mini da fushi,

Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.

12 Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini,

Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto.

13 “’Yan’uwana sun yashe ni,

Na zama baƙo ga idon sanina.

14 Dangina da abokaina sun tafi.

15 Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni.

Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa.

16 Sa’ad da na kira barana, ba ya amsawa,

Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni.

17 Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina,

‘Yan’uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.

18 ‘Yan yara sukan raina ni su yi mini dariya sa’ad da suka gan ni.

19 Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama,

Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana.

20 Fatar jikina ta saki, ba ƙarfi,

Da ƙyar na kuɓuta.

21 Ku abokaina ne! Ku ji tausayina!

Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa.

22 Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi?

Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba?

23 “Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa,

Ya rubuta shi a littafi!

24 Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse,

Ya rubuta su don su tabbata har abada!

25 Amma na sani akwai wani a Samaniya

Wanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.

26 Ko da yake ciwo ya riga ya cinye fatata,

A wannan jiki zan ga Allah.

27 Zan gan shi ido da ido,

Ba kuwa zai zama baƙo a gare ni ba.

“Zuciyata ta karai saboda ku mutane kun ce,

28 ‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?’

Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini.

29 Amma yanzu, sai ku ji tsoron takobi,

Ku ji tsoron takobin da yake kawo hasalar Allah a kan zunubi.

Don haka za ku sani akwai wani mai yin shari’a.”