AYU 32

Jawaban Elihu

1 Mutanen nan uku sun daina ba Ayuba amsa, saboda yana ganin kansa adali ne.

2 Sai Elihu, ɗan Barakel, mutumin Buz, daga cikin iyalin Arama, ya husata, yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, bai bari Allah ya baratar da shi ba.

3 Yana kuma fushi da abokan nan uku na Ayuba, domin sun rasa amsar da za su ba Ayuba, ko da yake sun hurta Ayuba ne yake da laifi.

4 Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.

5 Sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da wata amsa da za su ba Ayuba, sai ya yi fushi.

6 Elihu ɗan Barakel, mutumin Buz, ya fara magana, ya ce,

“A shekaru dai ni yaro ne ku kuwa manya ne,

Don haka ina jin nauyi,

Ina kuma jin tsoro in faɗa muku ra’ayina.

7 Na ce wa kaina, ‘Ya kamata kwanaki su yi magana,

Yawan shekaru kuma su koyar da hikima.’

8 Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum,

Yakan ba mutane basira.

9 Ba tsofaffi ne masu wayo ba,

Ba kuma masu yawan shekaru kaɗai yake gane abin da yake daidai ba.

10 Don haka na ce ku kasa kunne gare ni,

Bari in faɗa muku nawa ra’ayi.

11 “Ga shi, na dakata na ji maganarku,

Na kasa kunne ga maganarku ta hikima,

Tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa.

12 Na kasa kunne gare ku sosai,

Amma ko ɗaya ba wanda ya kā da Ayuba.

Ba kuma wanda ya ba shi amsar tambayarsa.

13 Ku lura kada ku ce kuna da hikima,

Allah ne kaɗai yake da iko ya kā da shi, ba mutum ba.

14 Ba da ni Ayuba yake magana ba,

Saboda haka ba zan amsa masa da irin amsarku ba.

15 “Abin ya cika musu ciki, ba su ƙara amsawa ba,

Wato ba su da ta cewa.

16 Ni kuma sai in tsaya don ba su ce kome ba?

Sun tsaya kurum, don ba su da ta cewa?

17 A’a, ni kuma zan ba da tawa amsa,

In kuma faɗi ra’ayina.

18 Cike nake da magana,

Ruhun da ka cikina ya iza ni.

19 Ga zuciya tana kama da ruwan inabin da ba shi da mafitar iska,

Kamar sabuwar salkar ruwan inabi wadda take shirin fashewa.

20 Tilas in yi magana don in huce,

Dole in ba da amsa.

21 Ba zan yi wa kowa son zuciya ba,

Ko kuma in yi wa wani fādanci.

22 Gama ni ban iya fādanci ba,

Idan na yi haka kuwa

Mahaliccina zai kashe ni nan da nan.”