AYU 39

1 “Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa?

Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?

2 Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu?

Ka san lokacin haihuwarsu?

3 Ka san lokacin naƙudarsu, sa’ad da suke haihuwar ‘ya’yansu,

Lokacin da ‘ya’yansu suke fita cikinsu?

4 ‘Ya’yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,

Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.

5 “Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so?

Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,

6 Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,

Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?

7 Yakan yi wa hayaniyar birane ba’a,

Ba ruwansa da tsawar masu kora.

8 Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa,

A can yake neman kowane ɗanyen abu.

9 “Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki?

Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?

10 Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya?

Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka?

11 Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?

Za ka kuma bar masa aikinka?

12 Ka gaskata zai komo,

Ya kawo maka hatsi a masussukarka?

13 “Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma!

Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.

14 Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta,

Ta bar ƙasa ta ɗumama su.

15 Takan manta wani ya iya taka su su fashe,

Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.

16 Takan yi wa ‘ya’yanta mugunta,

Sai ka ce ba nata ba ne,

Ko da yake ta sha wahala a banza,

Duk da haka ba ta damu ba.

17 Gama Allah bai ba ta hikima ba,

Bai kuwa ba ta fahimi ba.

18 Amma sa’ad da ta sheƙa a guje,

Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.

19 “Kai ka yi wa doki ƙarfinsa?

Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza?

20 Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango?

Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro.

21 Yakan yi nishi a fadama,

Yana murna saboda ƙarfinsa,

A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.

22 Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba.

Ba ya ba da baya ga takobi,

23 Kibau na ta shillo a kansa,

Māsu suna ta gilmawa a gabansa.

24 Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa,

Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.

25 Sa’ad da aka busa ƙaho yana ce, ‘Madalla.’

Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu.

26 “Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi,

Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu?

27 Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi sama

Ta yi sheƙarta can ƙwanƙoli?

28 A kan dutse take zaune, a can take gidanta,

Cikin ruƙuƙin duwatsu.

29 Daga can takan tsinkayi abincinta

Idanunta sukan hango shi tun daga nesa.

30 ‘Yayanta sukan tsotsi jini,

A inda kisassu suke, can take.”