ESTA 4

Esta Ta Ta Yi Roƙo don Mutanenta

1 Da Mordekai ya ji dukan abin da aka yi, sai ya yage tufafinsa, sa’an nan ya sa rigar makoki, ya zuba toka a kā. Ya fita zuwa tsakiyar birni, yana ta rusa kuka da ƙarfi.

2 Ya tafi kusa da ƙofar sarki, gama ba a yarda wani ya shiga ƙofar sarki da rigar makoki ba.

3 A kowane lardi inda aka kai umarni da dokar sarki, Yahudawa suka yi babban baƙin ciki, da azumi, da kuka, da makoki. Waɗansu da yawa da rigunan makoki a cikin toka suka kwanta.

4 Sa’ad da kuyangin Esta da bābāninta suka tafi suka faɗa mata abin da Mordekai yake yi, sai sarauniya Esta ta damu ƙwarai, ta aika da riguna a sa wa Mordekai, ya tuɓe rigar makokinsa, amma Mordekai ya ƙi, bai yarda ba.

5 Sai Esta ta kirawo Hatak, ɗaya daga cikin bābānin sarki, wanda aka sa ya yi mata hidima, ta aike shi wurin Mordekai, don ya ji abin da ya faru, har ya sa yake yin haka.

6 Hatak kuwa ya tafi wurin Mordekai a dandalin birnin, a gaban ƙofar sarki.

7 Sai Mordekai ya faɗa masa dukan abin da ya faru da shi, da yawan ƙudin da Haman ya ce zai biya a sa a baitulmalin sarki don a hallaka Yahudawa.

8 Mordekai kuma ya ba Hatak takardar dokar da aka yi a Shushan don a hallaka Yahudawa domin ya tafi ya nuna wa Esta ya sanar da ita, ya kuma umarce ta ta tafi wurin sarki don ta roƙi arziki ga sarki saboda mutanenta.

9 Sai Hatak ya tafi, ya faɗa wa Esta abin da Mordekai ya ce.

10 Esta kuma ta yi magana da Hatak sa’an nan ta aike shi da saƙo a wurin Mordekai cewa,

11 “Dukan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, ba tare da an kira shi ba, to, doka ɗaya ce take kan mutum, wato kisa, ko mace ko namiji, sai dai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don ya rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”

12 Hatak ya tafi ya faɗa wa Mordekai abin da Esta ta ce.

13 Sai Mordekai ya ce masa ya je ya faɗa wa Esta haka, “kada ki yi tsammani za ki tsira a fādar sarki fiye da sauran Yahudawa.

14 Gama idan kin yi shiru a irin wannan lokaci, to, taimako da ceto za su zo wa Yahudawa ta wata hanya dabam, amma ke da gidan iyayenki za ku halaka. Wa ya sani ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan maƙami?”

15 Sa’an nan Esta ta ce masa ya je ya faɗa wa Mordekai cewa,

16 “Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa’an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”

17 Sai Mordekai ya tafi ya yi abin da Esta ta umarce shi.