ESTA 6

Haman Ya Girmama Mordekai Tilas

1 A wannan dare kuwa sarki ya kasa yin barci, sai ya umarta a kawo littafin da aka rubuta al’amuran da suke faruwa don tunawa. Aka kuwa kawo, aka karanta wa sarki.

2 Sai aka tarar an rubuta yadda Mordekai ya gano maƙarƙashiyar Bigtana da Teresh, biyu daga cikin bābāni na sarki, masu tsaron ƙofa, waɗanda suka yi niyya su kashe sarki Ahasurus.

3 Sai sarki ya ce, “To, wace irin daraja ko girma aka ba Mordekai saboda wannan?”

Barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce, “Ba a yi masa kome ba.”

4 Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?”

Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.

5 Barorin sarki suka ce, “Ai, Haman ne yake tsaye a shirayi.”

Sai sarki ya ce ya shigo.

6 Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?”

Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”

7 Sai Haman ya ce wa sarki, “Abin da za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka ke nan.

8 Bari a kawo rigunan sarautar da sarki ya taɓa sawa, da dokin da sarki ya taɓa hawa, a kuma sa kambin sarauta a kansa.

9 Sa’an nan a ba ɗaya daga cikin manyan sarakunanka rigunan ya sa wa wanda kake so ka ɗaukaka, ya kuma hawa da shi kan dokin, sa’an nan ya zagaya da shi a dandalin birni, yana shelar a gabansa yana cewa, ‘Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.’ ”

10 Sai sarki ya ce wa Haman, “Yi maza, ka ɗauki rigunan da dokin, ka tafi wurin Mordekai, Bayahuden nan, wanda yakan zauna a ƙofar sarki ka yi masa kamar yadda ka faɗa. Kada ka kasa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”

11 Haman kuwa ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sa wa Mordekai riguna, ya hawar da shi kan dokin, ya zagaya da shi a dandalin birnin, yana cewa, “Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.”

12 Sa’an nan Mordekai ya koma ƙofar sarki, Haman kuwa ya gaggauta zuwa gidansa, yana baƙin ciki, kunya ta rufe shi.

13 Da ya koma gida, sai ya faɗa wa Zeresh, matarsa, da dukan abokansa, duk abin da ya same shi. Sai mutanensa masu hikima da Zeresh, matarsa, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara faɗuwa a gabansa, in dai daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, amma hakika za ka fāɗi a gabansa.”

14 Suna magana ke nan, sai bābānin sarki suka iso, suka tafi da Haman a gaggauce zuwa wurin liyafar da Esta ta shirya.